Yadda Abacha ya bani kyautan dala miliyan 2 – Rawlings
Tshon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya bayyana cewa ya taba shiga halin matsi na rashin kudaden yin ayyuka, sai tshon shugaban kasan Najeriya na mulkin soja Janar Sani Abacha ya kawo mai dauki alhali bai taba tsammanin shi Abachan zai taimaka masa ba. Amma kuma tallafin ya jawo cecekuce a kasar Ghana wanda ma har ya jawo masa bakin jinni.
Abacha
Rawalings ya ce Abacha ya bashi tallafin dala miliyan 2 ta hannun Gwarzo, amma daga baya aka dinga zargin wai kudin sun kai dala miliyan 5, a yayin wata hira da Jaridar Guardian Rawlings ya zayyana yadda lamarin ya kasance filla filla, yace wani mutum mai suna Gwarzo ne ya kawo masa makudan kudin a cikin wata karamar akwatin hannu kuma ya amsa. Amma ya karyata yamadidin da akeyi na cewa kudin sun hauran ma dala miliyan 5, ya kara da cewa gaskiyane kudaden sun zo mai a lokacin da yake cikin tsananin bukatansu don yin gudanar da manya manyan ayyuka.
A cewarsa “abin da nake so a lura dashi a nan shine a wannan lokacin muna cikin shirye shiryen tsaida mulki bisa kundin tsarin mulki. Muna butakatan kudi don gudanar da tarurrukan kuma mun samu gudunmuwa daga wurare kalilan. Abin burgewan shine ban taba zuwa na roki Abacha ba, ko in nemi gudunmuwarsa ba. Wannan shine abinda ya burgeni da shi. Ko kwandala ban tambayeshi ba. “sai dai kawai ya fahimci halin da muke ciki ne sai ya turo min da karamin akwatin kudi. Ina ganin motoci biyu ko uku aka turo su nemo ni a tashar jirgi na sojan sama”
“zan tashi ne a wannan ranar ta tashar sojojin sama sai ga wani mutum yazo ya same ni, lokacin da ya fada min yaza da sako daga Abacha sai na fasa tafiyar tawa, su kuma sai suka jirani. Ina biye dasu a cikin motata har muka isa otel, da fitar mu har zamu hau sama sai wannan mutumin mai suna Gwarzo ya baiwa wani mataimakinsa umarnin ya dauko wani karamin jakan kudi daga gidan sa kayan wata mota wato boot, da yake na fahimci menene a cikin akwatin, don haka sai nace masa: ‘barshi, rufe boot din, mu hau sama dakina muyi magana’.
Sai yace min yazo min da sako daga Abacha. “abu biyu kawai na fada: ‘ina da labarin ku ba kwa baiwa mutane tallafi sai kun sanar ma duk duniya, har ma kuyi kari’. “shiru kawai yayi yana kallona. Na biyu sai nace: ‘kar kayi tunanin idan ka bani koma menene zaka bani ba zan caccake ku ba idan kuka yi ba daidai ba.’ “bude bakinsa ked a wuya sai yace ‘Yallabai, muna bukatan ka fiye da yadda kake bukatan mu’. Wannan shine abinda ya fada. Bai yi maganganu da yawa ba, mutum ne mai mutunci, shiru shiru kuma ya manyanta, daka gan shi kasan abin girmamawa ne.
“a takaice dai, maganan da yayi sai yasa jikina yayi sanyi. Sai nace mai ba komai, zai iya aikawa a dauko sakon. Mataimakin nasa sai yaje ya kawo sakon: dala miliyan 2 sababbi daure cikin leda, masu nauyi. A nan muka bar su a falon dakin.”
Ya kara yan cewa “nan dai muka yi raha sai ya wuce. Na sanar da wasu daga cikin abokan aiki na maganan sakon Abacha. “na baiwa mutane biyu kusn dala duku 300 da hamsin-350,000 don aikin gaggawa. “an baiwa wani daga cikin manyan jami’an gwamnatin mu da yake gudanar da wani aiki na musamman wasu kudade dag cikin kudin.
Haka muka ci gaba har kudin ya kare. “bayan mutuwan Abacha, sai kasar ku ta fara gudanar da bincike kan kadarorin sa, na karanta a daya daga cikin jaridun ku cewa wannan mutumin kirkin Gwarzo ya ce wai dala miliyan 5 ya kawo min. nayi farin ciki da haryanzu nake rike da akwatin nan. “nayi matukar kaduwa da har irin wannan mutum mai mutunci zai yi irin wannan magana. Adadin kudin daya bayyana ya bani mamaki matuka. Da har zai iya zuka irin wannan karyan.
Bugu da kari ma bani da wani asusun ajiya nawa da zan sa wadannan kudaden. Asali ma muna bukatansu ne don biyan wasu bukatun kasar mu. “cikin ikon Allah, shekaru aru-aru bayan na samu sabani da wasu daga cikin abokan aikina, sai biyu daga cikinsu suka rubuta wani littafi akan zaben majalisan rukuni da kuma shirin gyaran fuskan gwamnati, kuma suka sanya cikin littafin wani abu mai kama da cewa Gwarzo ya bani dala miliyan 5 duk don su bata min suna. “nayi bakin cikin wai Gwarzo ne zai yi haka. A shirye nake a bincike ni ko karya nakeyi. Kila dama abin da yake so kenan.
“lokacin da janar Abdulsalam Abubakar ya hau mulki, na fada mai ya kula da kyau, cewa rahoton da ke yadawa a jaridu akan dala miliyan 5 ba gskiya bane, dal miliyan 2 ne ba 5 ba. Bai ce komai ba. “ Obasanjo ma daya hau mulki, haa na fada mai don ganin mu kashe maganan. Amsan da ya bayar shine: ‘gaskiya ne, dama haka suke, idan aka basu sako su kai ma wani, sais u kwashe mafi yawancin kudin, kaso mafi tsoka’ abin da Obasanjo ya fada kenan.” “ban saba da irin abubuwan nan ba, daba don haak ba aid a na kira Abacha, ban jin ma na kira shi akan batun kudin. “dana sani na kira shin a mai godiyan dala milyan 2, wata kila da ya ja ma mutanen sa kunne.
Ka fahimci abinda nake nufi? “ban saba da ganin kudi na yawo sama da kasa ba, kudi baa bin da ya dame ni bane. Haka ne, kasarmu talakar kasa ce, amma muna aiki dare da rana muga mun kawo gyara, mun sa kasar mu akan turba mikakkiya don ganin tattalin arzikin kasan ya habbaka. “muna da kima da mutunci,wand kuma ba zamu wulakantar dashi ba akan kudi kalilan.”
The post Yadda Abacha ya bani kyautan dala miliyan 2 – Rawlings appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.