Manyan labarai da suka fita a talata
Ma’aikatan Naij.com sun zakulo muhimman labaran da suka fita a ranar talata 12 ga watan yulio. Gasu nan kamar haka.
1. Rigima a majalisat dattijai: za’a tsige Buhari, Melaye yayi barazanan yi wa matar Tinubu dukan tsiya. Sanatoci sunyi barazanar tsige shugaba Buhari kamar yadda kafan watsa labarai na Sahara ta fitar.
2. Tasgerun Neja Delta sun fitar da hotunan harin da suka kai, sunci alwashin zasu ba Najeriya mamaki da harin sun a gaba
3. Saraki da ministan Shari’a sa labule don tattauna na musamman a ofishin Saraki
4. Ga wata babbar mace da ta ziyarci shugaba Buhari. Shugaba Buhari ya kar bakwancin daraktan yankin Afirka ta kungiyar lafiya ta duniya Dr Matshidiso Rebecca Moeti a fadar gwamnati
5. Katankatana: shin an gano wanda ya kashe paston cocin Redeem? Matsalar tsananta addini na kawo barazana kasancewar Najeriya kasa daya. kisan wata matar pasto mai suna Eunice Elisha ya janyo maganganu game da irin aika aikan da ake aikatawa da sunan addini. Me ya kamata gwamnatin Najeriya tayi dangane da wannan matsalar da ka iya jawo tashin hankali?
6. Pasto Adeboye ya jajanta wa iyalan paston da aka kashe a Kaduna. Shugaban cocin Redeem ya kai ziyaran ta’aziya ga iyalan Eunice Olawale a ranar litinin 12 ga watan yulio
7. Akwai Fargaba a cikin jam’iyar APC inda ake ganin mutane da yawa zasu bar jam’iyar saboda shari’ar Saraki. A wani rahoto da jaridar New telegraph tayi ta ce akwai fargaban cikin jam’iyan APC na ganin dumbin manyan yayan jam’iyan na shirin barin ta.
8. Fulani makiyaya sun sake kai hari, mutum 11 sun mutu. An rasa rayuka 11 a wani mummunar fada da ya afku tsakanin Fulani makiyaya da gwarawa a jihar Neja.
9. Ga abinda mata ke daurawa maimakon rigan mama
Wani sabon salo da ya fito yanzu kuma ya yawaita tsakanin yan mata shine yan mata sai su dinga daukan kif suna rufe mamunansu dashi a maimakon rigan mama da aka sani
10. Tsagerun Neja Delta sun ce ba zasu bari a fitar da mai kasashen waje ba. Yan tada kayar baya na Neja Delta sun sake fasa wani bututun main a kamfanin Exxon mobil mai suna Qua Iboe 48 wanda ke dauke da danyen man fetur da ake fitarwa kasashen waje. Tsagerun sunce “wai sai yaushe kamfanin main a kasashen waje zasu fara jin magana ne? mu ba zamu bari a fitar da mai ba”
The post Manyan labarai da suka fita a talata appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.