Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Buhari Ya fara tattaunawa da tsagerun Niger Delta- Boroh

0

-Mataimakin Buhari kan al’amarin Niger Delta ya bayyana cewa gwamnati na tattaunawa tare da yan bindiga

-Ya kuma bayyana dalilin da yasa Niger Delta Avengers bazasu kasance wani bangare daga cikin shirin afuwa ba

Paul Boroh

Brig.-Janar Paul Boroh (mai ritaya), mataimakin shugaban kasa kan al’amarin Niger Delta kuma mai tafiyar da shirin afuwa, ya sanar da cewa gwamnati ta fara tattaunawa tare da yan bindiga.

Ya ba da bayyani cewa ana magane ta hanyar kungiyar tattaunawa tare da duba ga yawan hare-haren bututun mai a yankin.

A cewar sa, hukumomin Najeriya basu shirya kawo tsagerun Niger Delta cikin shirin afuwa ba, hadi da Niger Delta Avengers.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya dau mataki kan sabon harin kisa a jihar Benue

Boroh yayi Magana ne a wani shirin talabijin da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja. Mataimakin shugaban kasar ya tatacce cewa an umarce shi da shigar da tsofafin mayaka 30,000 kawai cikin shirin, kuma bazai iya wuce haddi ba gurin kawo wasu mayaka.

Tsagerun Niger Delta Avengers sun fara barazanarhare-hare ne a farkon shekara ta 2016.

Tun watan Mayu, gas da kampanonin mai suka dunga fuskantar yawan harin bam, wanda ya yanke samar da mai a Najeriya daga bututu milliyan2.2 zuwa milliyan 1.5 a ko wace rana.

A farko shugaban kasa Buhari ya mayar da martani da lafazi mai tsauri, cewa kasar Najeriya zata yi maganin yan bindiga tare da mayakan Boko Haram- amma a yanzu ta koma rokon maharani kan su daina karya tattalin arziki.

The post Buhari Ya fara tattaunawa da tsagerun Niger Delta- Boroh appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса