Tsagerun Neja Delta sun sake fasa bututun mai
-Tsagerun neja delta sun sake fasa bututun man fetur da ake fitar wa kasar waje.
Kakakin kungiyar Tsagerun Neja deltan Birgediya janar Mudoch Agbinibo ya ce su ne da allhakin fasa bututun man a wata jawabin da Jaridar NAIJ.com ta samu.
bututun mai ya kama da wuta
Kungiyar Tsagerun Neja Deltan suka ce : “ Misalin karfe 7:30na yamma, kungiyar Tsagerun Neja Delta sun fasa bututun man kamfanin Exxonmobil Qua iboe 48 ,ta fitarwa kasar waje. Wai shin yaushe kamfanonin man kasar waje zasu saurare mu ne, munce babu fitar da mai.”
Amma,kakakin kamfanin exxonmobil, todd spitler, yace babu harin da aka kai kafufuwan man su. Yace: “babu wani harin da aka kai kafufuwan man fetur dinmu”
Tsagerun neja deltan sun kai hare-hare da dama akan kafufuwan man fetur da gas kudancin najeriya tun watan fabrairun shekaran nan. Kungiyar na ikirrarin cewa a kara kason kasafin kudin mutanen yankin saboda arzikin yankin su ne aka rabarwa mutanen kasa.
KU KARANTA : Tsagerun Neja Delta sun sake fasa bututun mai
Sanadiyar hare haren da Tsagerun Neja Delta ,sarrafa man feturin najeriya ya sauko ganga 600,000 a rana sabanin 2.2 miliyan a rana da ake sarrafawa a da.
The post Tsagerun Neja Delta sun sake fasa bututun mai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.