Kungiyar Igbo ta bayyana yanda Buhari ya mayar da Kanu
-Kwanan nan yan Najeriya suka kara kaimi kan cewa a mayar da kasar zuwa jumhuriyyar gaskiya
-Kungiyar Igbo Youth Movement (IYM) sun bayyana cewa a yayin da aka la’antar Nnamdi Kanu wadda a ka tsare kan zargin cin amanar kasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da shi gwarzo a kaikaice.
-Kungiyar IYM sun yi kira ga shugaban kasa da ya daina ‘Murkushe su’ dabaru kan kungiyar IPOB da sauran mayaka, a maimakon haka ya mayar da hankalinsa kan yadda zai gyara kasar
kungiyar IPOB
Yayin da kira kan gyara kasar Najeriya ya yawaita a fadin Najeriya, kungiyar Igbo Youth Movement (IYM) sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mayar da Nnamdi Kanu gwarzo, shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB).
Nnamdi Kanu na hannun hukuma kan zargin cewa ya ci amanar kasa tare da mabiyan sa gurin kokarin su na ganin cewa Kabilar Igbo ta balle daga Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tayi gargadi ga makaratun jami’a kan dalibai
Kungiyar sun tunasar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa tsegumin Kanu ya fara samun karbuwa a fadin kasar Najeriya tare da kira kan cewa a gyara kasar zuwa jumhuriyyar gaskiya.
A wata sanarwa da aka bayar bayan bikin al’ada na shekara-shekara karo na 17th da akayi a jihar Enugu, kungiyar sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fara gyara kasar nan da nan, kuma ya daina murkushe su.
Kungiyar IYM sun bayyana cewa ci gaba da tsare Kanu da ake yi ya mayar da shi gwarzo.
The post Kungiyar Igbo ta bayyana yanda Buhari ya mayar da Kanu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.