Takaici ke tayar da kayan bayan takin neman Biyafara – APGA
–Shugaban jami’ayyar APGA ta kasa, Chif Victor Oye yace Abinda ke tayar da kayar bayan yakin neman biyafa zai yi sauki idan aka daina zalunci da rashin adalci ga kabilan Igbo.
–Yace rashin raban dai dai na arzikin kasa ga kabilan Igbo ke jawo haka.
–Ya kara da cewa halin hanyoyi mota a yankin kudu maso gabashin kasan da kuma rabon mukamai da akeyi a kasar ke tayar da kayar bayan.
Jam’iyyar APGA tace takaicin rashin adalci da mawuyacin halin da mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya ke ciki ke kara hura wutan tayar da kayar bayan yakin neman Biyafara a kasa.
Chief Victor Oye,APGA
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa, shugaban jami’yyar APGA ta kasa, Chif Victor Oye, ya bayyana ma manema labarai a ranar talata,12 ga watan yuli cewa tayar da kayan bayan da kungiyar Indigenous People of Biafra, (IPOB) da Movement for the Actualisation of the Sovereign State of Biafra, (MASSOB) keyi, zai ragu idan gwamnati ta daina kebance yan kabilan Igbo a kasar.
Yace : “Shi dan Igbo bai yi imani da lalata ba. Sun sha bakar azaba lokacin yakin Biyafara wanda har yanzu basu gama farfadowa ba. Suna son gamayyar Najeriya, Amma rashin daidai da akeyi wajen rabon arzikin kasa ne ke sa su tayar da hankali. Muddin aka daina zaluncin da nuna son kai, duniya zata gane cewa mutanen kabilan Igbo na son zaman lafiya.
Idan aka gina masu hanyoyi masu kyau,aka sama masu aiki, aka basu mukamai masu kyau, zasu daina tayar da kashin baya. Idan aka gyarabhanyoyin Onitsha – Enugu , Oba – Nnewi – Okigwe , Aba – Port Harcourt , Owerri – Port Harcourt , Enugu – Umuahia – Aba, kuma aka fara dai dai wajen raba mukamai a kasa, zasu daina.”
KU KARANTA : Peter Obi ya karyata tsawatarwan da Ekwueme ya masa
A bangare guda, cigaba da tayar da kayar bayan neman biyafara ya sanya shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada wata kwamiti domin dubi cikin al’amarin da ke faruwa da kuma haduwa da kungiyoyin tayar da kayar bayan musamman Movement for the Actualization of Sovereign State of Biafra (MASSOB), da Indigenous People of Biafra (IPOB).
Game da Jaridar The Sun, Shugaban kasa, a makonnin baya ya kira wani taro da manyan mutane irinsu tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da manyan ma’aikatan gwamnati suka halarta domin tattaunawa akan al’amarin.
The post Takaici ke tayar da kayan bayan takin neman Biyafara – APGA appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.