Ana sayar da $1 kan N356 a kasuwannin bayan fage
Yanzu haka dai rahotannin dake zuwa mana suna nuna cewa darajar kudin Naira ta fadi a karon farko cikin satin nan a kasuwannin bayan fage
Dollar
Wannan ya faru ne dangane da rahoton da muka samu na cewa yanzu haka ana saida duk $1 akan kudin N356 ba kamar yadda yake ba a jiya talata inda ake saida ta a N353. An samu karin N3 kenan. Kudin Naira din sun dan yi daraja kadan kafin tafiya hutun sallah inda aka rika saida $1 akan N352 kafin daga baya ya koma N353. To yau kuma da aka tashi sai aka ga har ta kai N356.
A ta bakin wani mai harkar canjin kudin, yace wannan faduwar darajar Naira din bai rasa nasaba da yadda karancin $ din ke kara addabar kasar. Ya kuma ci gaba da cewa: “babu kudin $ din kuma sannan babban bankin Najeriya baya saida mana. Idan CBN din ya fara saida mana kudaden $ din akwai yiwuwar darajar Naira din ta karo.”
The post Ana sayar da $1 kan N356 a kasuwannin bayan fage appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.