Diyar Abacha ta yi ma wani da ya zageta addu’a
– Kai! Yan Najeriya basu da sauki.
– Gumsu Sani Abacha diyar tsohon shugaban kasar nan Gen. Sani Abacha ta je a shafin ta na sada zumunta inda take taya kakakin majalisar dokokin Najeriya Hon. Yakubu Dogara.
Amma zancen bai tsaya nan ba inda wani can wanda abun bai shafa ba mai suna Timi Ayodele ya nuna rashin jin dadin sa a kan ta. Shi dai wannan dan Najeriyar sai yaje ya zageta inda yace mata murnar me zata taya shi bayan mahaifinta shine ya jefa kasar nan cikin duk halin da take ciki sa.
Ya kuma kara da cewa duk tabargazar da mahaifin nata yayi har yanzu ba’a gama magance ta amma tazo tana yi ma wani murna.
Ita kau sai ta bashi mamaki inda ta bashi amsa ba irin tasa ba kuma ba cikin fushi ba. Sai kawai tayi masa addu’ar Allah ya shirya shi. Har ma kuma ta kara da bashi shawarar me zai hana ya fito takara a zabe mai zuwa don ya bada gudummuwar sa wurin ci gaban kasar nan.
Ga dai yadda muhawarar tasu ta kasance nan kasa:
The post Diyar Abacha ta yi ma wani da ya zageta addu’a appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
