Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Tsagerun Neja Delta sun sanar da tsagaita wuta na sati 2

0

Daya daga cikin masu tada kayar baya na yankin Neja Delta sun sanar da tsagaita wuta har na tsawon sati 2 tare da ba shugaba Buhari shawarar ya canza nunanin shi game da kin tattaunawa da su

Niger Delta Avengers

Tsagerun dai suna amsa sunan Niger Delta Revolutionary Crusaders (NDRC) kuma suna zaune ne a jihar Bayelsa. Mai magaba da yawun su Woi Izon-Ebi, yace: “Bayan mun tsaya tsaf mun kula da yadda lamura ke tafiya tare kuma da duba ga yadda mutane ke sa baki don ganin an samu dai-daito, to yanzu haka mu muna sanar da cewa zamu tsagaita wuta har na tsawon sati 2 don mu bada damar tattaunawar”.

“A cikin wannan lokacin muna son gwamnatin tarayya da ta tattauna da wasu amintattun mu, sarakunan mu da ma shugabannin al’ummar mu. Gwamnatin muna so ta yi watsi da karnukan siyasar da suke zuwa Abuja su zo nan Neja Delta.”

“Idan kuma har lokacin ya wuce ba tare da wani hunkuri daga gwamnati ba, to tabbas babu yadda zamuyi sai dai mu dawo da ayyukan mu har sai mun ga gwamnati ta bar anfana da arzikin mu.” “Don haka muna kira da shugaba Buhari ya fito fili ya bayyana kudurorin sa a kan mu sannan kuma dole ne ya sa cigaban mu a gaba.”

“Dole ne gwamnati ta fifita cigaban yankin mu fiye da na kowa. Sheka ru 50 kenan muna wahala.” “Yanzu bukatun mu basu wuce tsaftar muhalli ba, kyawawan hanyoyi, ruwan sha da dai duk sauran ababen more rayuwa.”

Wannan dai yana zuwa ne bayan da wasu gungun tsagerun na Neja delta suka kai hari a kan bututun man Exxon Mobile.

The post Tsagerun Neja Delta sun sanar da tsagaita wuta na sati 2 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса