Willian ya sabunta kwantaraginsa a chelsea
-Willian Borges ya sabunta kwantaraginsa na tsawon sheka hudu a chelsea.
– Dan shekara 27 ya sabunta kwantaraginsa wanda zai bashi daman zama a kungiyar har Sai 2020.
– Willian dindai shine dan wasan dayafi kowane dan wasa na gungiyar hazaka a wannan shekar acewar abokan wasan sa.
Willian Borges
Dan wasa Willian Borges ya sabunta sabon kwantiraginsa na tsawon shekaru hudu a kungiyar ta chelsea wanda zai bashi daman zama a kungiyar har Sai 2020. Dan shekaru 27 din kuma dan asalin kasar Brazil din andai zabeshine a kungiyar a karshen shekarar data gabata amatsayin dan wasan dayafi kowa kokari a kulob din wanda abokan wasan nasa suka zabeshi.
Willian din yace ” nayi murna Sosai dana sabunta kwantiragina da chelsea, abun alfaharine mutum yaci gaba da wasa a wannan kulob din gami da Karin shekaru hudu, kuma Zanyi duk Iya kokarina naga na taimaka ma kulob din sunci kofuna da dama. Abun mamaki ne a wajena tun sadda nazo chelsea shekaru uku da suka wuce, naci kyaututtuka gashi kuma shekarar Bara an zabeni dan wasan dayafi kowa kokari. Ina fata naci gaba da zama a matsayin ashekaru masu zuwa domin na samu cigaba a rayuwata”.
KU KARANTA : Kungiyar PSG na neman dan wani wasan Atletico Madrid
Willian dai yazo chelsea alokacin kakan wasanni a shekarar 2013 daga Anzhi makhachkala Bayan da yayi suna a shakhtar Donetsk. A shekarar 2014/2015, Ya taimaka ma kungiyar sunci capital one cup dakuma premier league a shekarar sa ta biyu. Yanzu haka willian ya bugama chelsea wasa 140, yaci kwallaye 19.
The post Willian ya sabunta kwantaraginsa a chelsea appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.