Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Gwamnatin tarayya ta rarrashi kamfanonin mai

0

-Minista Ngige ya roki kamfanonin mai kan korar ma’aikata

-Najeriya na cikin tsaka mai wuya ta fuskar tattalin arziki

-Shugaban Kungiyar PENGASSAN ya ce za su janye yaji aikin da suke yi

Ministan Kwadago na Najeriya, Chris Ngige

Gwamnatin tarayya ta roki manya-manyan kamfanonin mai na kasar da cewa kar su kori ma’aikatansu, Sanata Ngige ministan kwadago ne ya yi wannan roko a ranar Talata 12 ga watan Yuli a wani taro da ya yi da shugabannin kungiyoyin kwadago na PENGASSAN da NUPENG da kuma manyan ma’aikatan kamfanonin mai na kasa da kasa.

An shirya taron ne don sasanta tsakanin kungiyoyin kwadagon biyu da kuma kamfanonin mai kan zargin cewa kamfanonin na shirin korar ‘ya ‘yan kungiyar da ke aiki da su, a inda ya ce hakan shi ne mataki na karshe da yakamata su dauka a halin da ake cikin na matsin tattalin arziki a kasar.

KU KARANTA: Hausawa ba sa kyamar ‘yan Igbo – Sarki Sunusi

Manyan kamfanonin man dai sun shirya sallamar ma’aikatan ne a bisa dalilin na zaman kashe wando, a inda ministan ya nuna musu cewa su sake duba dokokin kwadago da kuma tanade-taneden dokar musamman yadda ta shafi rage ma’aikata a bisa dalilin zaman banza, ya kuma nuna musu illar rage ma’aikatar ya na mai cewa

“Idan ku ka raba mutane da aikinsu za su kara yawan marasa aiki a kasa, wanda kuma zai sa su iya zama barazana ga tsaro”.

A karshen taron, Mista Johnson Olabode shugaban kungiyar PENGASSAN ya godewa ministan ya kuma ce zai tattauna da ‘yan kungiyarsa domin janye yajin aikin da suke yi.       

  

The post Gwamnatin tarayya ta rarrashi kamfanonin mai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса