Kafafun yada labarai na kara ma aya zaki – Ortom
–Akwai alamun cewa rahotannin da ake yadawa a kafafun yada labarai akan batakashi tsakanin Fulani makiyaya da Manoma, ana kara ma aya zaki.
–Wannan shine abinda gwamnan Jihar Benuwe, Chif Samuel Ortom ya yanke.
–Ortom ya fadi hakan ne a ziyarar da ya kai ma Ministan harkokin cikin gida, laftanan janar Abdul Rahman Bello Dambazau (Mai ritaya).
Gwamnan Jihar Benuwe ya bawa kafafun yada labarai shawara cewa su daina kara ma aya zaki wajen yada hayaniyar fulani makiyaya da manoma. Gwamnan ya fadi hakan ne bayan wata ganawa da yayi da ministan harkokin cikin gida, Laftanan Janar Abdurahman Dambazau,akan abubuwan dake faruwa .
gwaman ortom tare da dambazau
Yayinda yake magana da manema labarai, gwamna Ortom ya baiwa kafafun yada labarai cewa su daina kara ma aya zaki akan al’amuran da suka shafi tsaro, musamman rigimar da ke maimatuwa tsakanin fulani makiyaya da manoma, kuma yace jami’an tsaro na iyakan bakin kokarinsu. Ya kara da cewa akwai masu laifi a cikin bangarorin biyu kuma gwamnatin sa zatayi iyakan kokarinta wajen kula da al’amarin.
Hakazalika, ya jaddada cewa akwai bukatan gwamnatin tarayya da gwamnatin Jihar Benuwe su hada hannu wajen kawar da irin wadannan abubuwan kuma hana sake dawowansu.
KU KARANTA : Buhari ya dau mataki kan sabon harin kisa a jihar Benue
Kwanan nan,kafafun yada labarai suka bada rahotannin harin da Fulani Makiyaya suka kai karamar Hukumar Logo da Ukum a Jihar Benuwe, cewa an kashe rayuka 81. Amma, kakakin jami’an yan sanda na Jihar Benuwe, ASP Moses Yamu, ya karyata rahotannin, ya ce mutane 22 kacal aka kashe.
Gwamnatin jihar Adamawa ta shirya filyen kiwo 30 a jihar.Game da kwamishanan cigaban kiwon dabbobi,Isa Salihu, kaddamar da filayen na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na kawo karshen fada tsakannin Fulani Makiyaya da Manoma.
The post Kafafun yada labarai na kara ma aya zaki – Ortom appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.