Magu ya yi gum a kan batun Buratai
-EFFCC na shan matsin lamba kan ta binciki yadda Buratai ya mallaki kadarori a Dubai
-Shugaban hukumar EFCC ya ki magana kan batun Buratai
-Ibrahim Magu ya ki amsa tambayar ‘yan jarida kan babban hafsan sojin Najeriya
Ibrahim Magu, shugabn hukumar EFCC
A wani lamari kamar wasan kwaikwayo a ranar Talata 12 ga watan Yuli, shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya ki amsa tambayar ‘yan jarida kan batun wasu gidaje da babban hafsan sojin Najeriya Tutur Buratai ya mallaka a Dubai.
A cewar jaridar PUNCH, bayan halartar wani taro na kwana daya kan yaki da cin hanci da rashawa wanda kwamiti mai ba shugaban kasa shawara kan cin hanci da rashawa, tare da kungiyar Lauyoyi suka shirya a Abuja, bayan shugaban hukumar ya fito, ya kuma tsaya don amsa tambayoyin ‘yan jaridu, da soma tambayarsa kan batun mallakar kadarorin Burutai, sai shugaban ya ki ya ce komai, ya kuma yi maza ya shiga motarsa ya bar wurin.
KU KARANTA: Iran ta matsa kaimi a kori Burutai
Wasu ‘yan Najeriya su na ta kire-kiraye kan cewa gwamnatin tarayya ta kori babban hafsan, ko kuma ya ajiye aikinsa kan mallakar wasu gidaje biyu da kudinsu ya kai Dala miliyan 1 da 500,000, a Dubai. Cikin masu wannan kiraye-kiraye har da Femi Falan wani babban Lauya.
Sai dai wata kungiya mai zaman kanta mai kira da samar da adalci, da daidaito, da kuma kawar da kumbiya-kumbiya (CESJET), ta ce, kiran da Lauya Falana ke yi na korar Buratai tamkar lauya ne ke fassara littafin Bible.
Tuni gwamnatin tarayya ta wanke babban hafsan, a inda ta ce ya sayi kadarin ne da guminsa ta hanyar tara kudin na tsawon lokaci, kuma ya bayyana kadarorin ga hukuma.
The post Magu ya yi gum a kan batun Buratai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.