Za mu soma kama baragubin Lauyoyi –Magu
-Shugaban hukumar EFCC ya koka da yadda wasu lauyoyi ke kawo cikas a yaki da cin hanci da rashawa a kasar
-Magu ya koka kan yadda ma’aikacin gwamnati ke iya fitar da miliyan 800 ya biya lauya kan shari’a
-Hukumar za ta kuma soma kame mutanen da barayin gwamnati ke amfani da su wajen boye kudin sata
Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC
A wani da jawabi da shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya yi a wani taro kan cin hanci da rashawa a Abuja, shugaban ya bayyana irin illolin da cin hanci da rashawa ya yiwa kasar nan.
KU KARANTA: EFCC ta gano N500 miliyan a asusun shugaban majalisa
A cewar rahotanni, shugaban EFCC ya yi ikirarin cewa hukumarsa za ta soma farautar baragurbin lauyoyi wadanda ke daurewa cin hanci da rashawa gindi ta hanyar tallafawa abokan huldarsu halarta kudin haram. Ya na mai cewa:
“Idan ka na halarta kudin haramta mu damke ka, kai babban lauya ne mai lambar SAN, ko kuma kai ne shugaban EFCC, babu ruwan doka, domin ba sani ba sabo.”
KU KARANTA: EFCC ta gano N2.5Miliyan a asusun ‘yar aikin gidan Minista
Shugaban na EFCC ya kara da cewa; “ Nan ba da dadewa ba za mu soma binciken yadda ake amfani da wasu mutane wajen sayen kadarori da kudin sata, da kuma yadda wasu ke taimakawa bata gari gujewa hukunci, sannu a hankali duk za mu kama su”.
Daga karshe Ibrahim Magu ya yi kira ga jama’a da su hada hannu da hukumar a yakin da ta ke yi da cin hanci da rashawa domin gadarwa da ‘yan Najeritya masu tasowa kasa ta gari
The post Za mu soma kama baragubin Lauyoyi –Magu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.