Abunda Mourinho yace akan Manchester, Old trafford
-Jose mourinho zai fara wasan sa na farko a gida 3 ga Watan Agusta.
-Jajirtaccen yayi bayani akan filin wasa na old trafford.
-Manchester United din dai zata kara da Everton.
Jose mourinho, sabon manajan manchester yace sauran kiris yafara gudanar da abunda ya kawoshi. Mourinho dai zai fara wasan sa na farko a manchester united a matsayin sa na manaja tare da dan wasan nan Rooney da kungiyar everton 3 ga wata Agusta.
Tsohon manajan Chelsea da Real Madrid din ya bayyana kosawar sa dangane da yadda akeciki inda yace ” abun tausayine, inama ace gobe ne za’afara saboda inata jiran lokaci yayi”. Dan shekara 53 ya Kara dacewa ” na dauki lokaci mai tsawo a harkar kwallon kafa kuma a mataki mai girma, saboda haka bana cikin damuwa da takura Ina cikin kwanciyar hankali kuma a shirye nake da wannan Aikin, amman naje filin wasan a matsayin managan manchester united, gaskiya wannan abun alfaharine.
Yaci gaba da cewar ” filin wasane dake da girma da zakayi tafiya harna tsawon mita 50 daga farko zuwa karshen fita. Wanda yasha banban da filayen wasannin dana tabayi.
Kulob din dana yi filayen wasannin nasu basu da irin wannan, su nasu a hade yake da filin wasa. Babu irin wannan wajan da zaka Iya Jin dadi ko rashin Jin dadi a filin wasa, kasan idan abubuwa sukayi kyau to zakaji dadi, haka kuma idan basuyi kyau ba bazakaji ba.
KU KARANTA : Arsenal sun amince su bada Giroud don sayen dan kasar Argentina
Mourinho ya Kara dacewa ” Ina ganin wannan wajan mai tsawon mita 50 kana tafiya zaisa na dauki wasu sakonni ina jinsa jikina.
Acewar manchester united din Wayne Rooney zaiyi wasan goyon baya a wasan farkon wannan shekaran tare da samar da hadinkai gamida samar ma gungiyar nan ta England captains foundation dake kula da yara marasa galihu dakuma marayu zunzurutun kudi har uro miliyan biyar.
The post Abunda Mourinho yace akan Manchester, Old trafford appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
