Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Bournemouth sun kafa tarihi na sayen Jordon

0

-Bayan da dan wasan ya kasance bai samun daman buga wasa a karkashin kochin liverpool din wato Jurgen Klopp, Jordan Ibe yabar kungiyar ta liverpool inda ya koma kungiyar bournemouth.          – Ibe yadai rattafama kungiyar ta Bournemouth hannun shekara hudu inya hakan ya zama abun tarihi a kungiyar na sayan dan wasa har yuro miliyan 15.      

  -Harma yaje ya samu abokan wasan sa a birnin Chicago dake USA domin yayi tirenin din buga wasan pre season.     

             

Jordon Ibe

     

Kungiyar Bournemouth din dai tayi dan wasa ne haifafen kasar Najeriya mai suna Jordon Ibe daga kungiyar liverpool akan kudi yuro miliyan15 da kungiyar ta kafa tarihi cikin akan Yan wasan da take saya. Ibe dake da shekara 20, yadai rataffa hannun shekara hudu inda zaiyi wasa a vitality sitadiyom wanda shine dan wasa na biyar da kungiyar suka saya a wannan shekaran.

Shugaban zantarwan na bournemouth yace sunyi farin ciki da kawo dan wasan kungiyar su. Inda yace, yayi wasa da dama a kungiyar ta liverpool a shekarar bara wanda tun a lokacin muke ta kokarin muga mun kawoshi kungiyar mu domin yaci gaba da wasa wanda zaisa yakai wani mataki da kowa zai sanshi, saboda yana da kwazo. Yanzu Dai mun sayi yan wasa guda biyar a wannan kakan wa’anda munasa ran zasuyi kwazo Sosai.

KU KARANTA :John Terry ne zai jagoranci Chelsea kakar wasa mai zuwa

Hakan ya nuna hikimar wannan kungiyar saboda daman muna shirin yin haka tuntuni wajan ganin munyi gyara kafin a fara buga gasar premier league. Dan wasan da yayima kasar ingila wasa na yan shekaru 21, kuma yayima liverpool din wasa guda 41 a dukkannin wasannin da suka buga na gasar premier league din shekarar data gabata, sannan kuma yayi wasa shida da ita kungiyar ta liverpool a wasannin da suka buga na europa league wanda Jurgen klopp din ya samu daman kaiwa wasan karshe.

Ibe wanda ya buga ma ingila wasa guda hudu na yan kasa da shekaru 21, yadai rattafama kulob din liverpool hannu na tsawon shekaru 5 a watan mayun shekarun data gabata, saidai kochin na liverpool Jurgen klopp baiyi wani wasa dashi ba sosai.

The post Bournemouth sun kafa tarihi na sayen Jordon appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса