Hugain Ya Fada Cewa Zai Tafi Juventus
-Dan kwallon gaban ya yanke shawarar barin Napoli.
-Hugain Ze tafi Kungiyar Juventus.
-Arsenal sunyi kokarin sayen dan wasan.
Gonzalo Higuain
Goal.com,Kungiyar Juventus sun yarda sayen dan wasan Napoli Ganzalo Higuain na tsawon shekaru 4 da albashi har €7million a shekara. A da munji cewa wakilin Ganzalo Higuain yace”Dan wasan baze kara sa hannu a kwantaragi ba da kungiyar Napoli,dan wasan na gaba ya jefa kwallo 36 a kakar wasar da ta gabata yayin da Napoli ta gama a matsayi na 2 bayan. Wadandaa suka lashe gasar kofin seria A Juventus. Sai dai wakilinshi ya bayyana cewa “Mun zo da tsari mai kyau na zuwa wasan zakarun turai,mu zama zakaru,mu bunkasa,amma kungiyar bata nuna za ta yi hakan ba,dan haka ya na da damar ya dena wasa da kungiyar,Amma kuma ze iya. Kin sabunta kwaantaraginshi in da zuwa 2018 ze iya zuwa duk in da ya gadama.
KU KARANTA : Nani ya koma kulub din Valencia
Goal sunce kungiyar Juventus suna kan gaba gurin sayen dan wasan amma da wuya in zasu iya cimma kudin da aka sallama shi €94million,sai dai suna da burin yin musaya da wani dan wasa dan su samu saukin biya,Majiya ta kara cewa darakatan kungiyar Juventus Gusseppe Marotta ze hadu da wakilan Napoli su tattauna kan cinikin kwanaki masu zuwa.
Manyan kungiyoyi sun yi zawarcin dan wasan. Sanannen dan jarida Gianluca Di Marzio ya rohoto cewa Arsenal tana shirye da ta bada Oliver Giroud ga kungiyar Napoli dan samun damar kawo Ganzalo Higuin Kungiyar.
The post Hugain Ya Fada Cewa Zai Tafi Juventus appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.