Majalisar dattawa na kitsa koron mataimakin PMB
– An ruwaito cewa sanatocin na kitsa korar mai taimakon Buhari, Ita Enang
– Suna kuma shirin dakatar da sanatoci shida a kan abin kunyar nan na jabu
– Enang yace bai yi wani laifin da hukumar majalisar zata kore shi ba
Sanatocin guda shida sune, Kabiru Marafa, Suleiman Hunkuyi, Ahmed Lawan, Ajayi Borofice, Gbenga Ashafa da Abdullahi Gumel.
Wani babban jami’in majalisar yace, shugabannin majalisar suna zargin su da cin amana, ya kara da cewa shi Enang na da zabi biyu, ko dai ya aje aikinsa sa’annan yaje ya bada sheda a kan shari’ar da akeyi, ko kuma a kore shi.
The post Majalisar dattawa na kitsa koron mataimakin PMB appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.