Ana zargin gagarumar almundahana a Aso Rock
– Wanda ya gano shine Major General Babagana Monguno, Mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan harkokin tsaro
– Shugaba Buhari ya dauki kusan shekara guda yana yakar wasu fitattun shugabannin kasar a kan cin hanci da rashawa
– Bayan wannan abin takaicin, wanda aka gano yayin da shugaba Buhari ya sa ayi biniken tantancewa, an kuma gano ma’aikatan karya guda 29 a aso rock
Babagana Monguno
Wani rohoto na mujallar Starconnect News wanda ba’a tantance shi ba na cewa an gano almundahana ta N4.0b daga cikin N6.5b da aka ware ma ma’aikatan tsaron fadar shugaba kasa
Mai bada shawarar ya rage kudin daga N6.5b zuwa N2.0b, abin da shugaban kasa ya yaba kuma ya amince da shi.
The post Ana zargin gagarumar almundahana a Aso Rock appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.