Dan ta’addan Direban da ya aikata ta’asa a Faransa
–Direban da kusa cikin jama’a da mota sunanshi Lahouaje Bouhel .
–Dan shekara 31 dan kasar Tunisiya ne.
–Yayi amfani da fasfot din Faransa da suna weird loner
–An kashe Direban motan da aka lura akwai bindigogi da nakiyoyi a cikin motan
Dan ta’addan yayi amfani da babban motan ya kashe akalla mutane 84 a raran bikin Bastille a Birnin Nice.
Game da cewar Jaridar Telegraph, dan shekaru 31 haifaffen kasan Tunisiya sunansa Lahouiej Bouhlel. An kiranshi da suna Weird Loner, mazaunin Riveria city, kuma ya kasance kangararre kafin yanzu. Ya dade yana saba dokoki.
A ranar Juma’a ,15 ga watan yuli Wata majiya a kasan Tunisiya tace dan ta’addan da ya kashe akalla mutane 84 da mota dan kauyen Msaken ne a kasar Tunisiya. Majiyar ta kara da cewa jami’an tsaron Tunisiyan basu san dan tsatsauran ra’ayi ba ne,kuma shekarun shi 4 raban da yaje kasar Tunisiyan. Majiya ta ce boulel na da aure da yara 3.
KU KARANTA : Dole ayi ma Najeriya garambawul – Cewar Gani Adams
Akalla kananan yara 3 ne suka rasa rayukan su a mumunan kisan da yayi. Daruruwa kuma na asibiti, musamman 18 da ke halin mutuwa yau ko gobe.
The post Dan ta’addan Direban da ya aikata ta’asa a Faransa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.