Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Kotun Abuja tayi watsi da neman belin Omisore.

0

–Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Osun ya cigaba da kasancewa a garkame a ofishin Hukumar Hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagwon kasa watau EFCC.

–Wata Kotu dake zaune a babban birnin tarayya, Abuja ,ta hana Omisore beli.

–Omisire tsohon dan takaran gwamnan Jihar Osun ne karkashin jam’yyar adawa PDP.

A yau ne 15 ga watan yuli Wata babban Kotu dake zaune a Abuja ta hana Sanata Iyiola Omisore beli. Omisore dan shekara 58, ya jemi beli a kotu bayan Hukumar EFCC ta damke shi akan zambar kudi biliyan N6bn .

Omisore yayi ikirarin cewa hukumar yaki da rashawan ta an take hakkin shi na dan Adam ,a wata kara da ya kai.

Lauyan Omisore, Chris Uche, ya fada a jiya ,14 ga watan yuli cewa umurnin da aka bada na damke shi da kuma garkame shi kama karya ne ba a bisa kundin tsarin mulki ba. Ya mika kokon baran sa ga kotun cewa ta baiwa Omisore beli kafin a gurfanar da shi,da kuma samu damar kawo shi kotun a ranar da wa’adin dakatar da karan ya kare. Lauyan Hukumar EFCC, Mr. Takor Ndifon ya ki abinda lauyan Omisore ya nema. Ya ce abi umurnin da kotu ta bada kawai.

KU KARANTA : FG ta kirkiro tawaga 20 domin yaki da Rashawa

Alkalin kotun, Jastis Olukayode Adeniyi ya yanke hukuncin cewa belin da Omisore ke nema ba zai yiwu ba, kawai ya jira kwanaki 14 da kotu ta yanke masa da ya kasance a garkame ta kare. Alkalin ya kara da cewa duk wani yunkurin ba da belin yanzu ,tafka da warwara ne. Tunda kotu ta yanke wani hukunci.

A farkon makon nan,Hukumar EFCC ta ce ta samu wasu takardun da suka cancanci bincike da aka samu a gidan Omisore, shi yasa Hukumar yaki da rashawan ta nemi gurfanar da shi.

The post Kotun Abuja tayi watsi da neman belin Omisore. appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса