Minista yayi bayani dangane da Nija Delta
– Minastan Harkokin Neja-Delta Usani Usani Uguru ya bayyana wadanda suke da hannu cikin rikicin Neja-Delta na Kasar
– Ministan wanda ya fito daga yankin na Neja-Delta, yayi hira da manema labarai kan harkokin yankin.
– Minista Usani Uguru ya bayyana abin da ya sani dangane da Niger-Delta Avengers
Niger Delta Avengers
Ga dai dan tsokaci daga hirar ta sa:
Tambaya: Ana tunani kamar dai ba a san yadda za a shawo kan matsalar yankin Neja-Delta ba, ya abin yake ci maka tuwo a kwarya?
Amsa: Ni ban yarda cewa ba a san yadda za a shawo kan wannan matsala ba sam. Babu abin da ubangiji ba zai iya ba. Akwai mafita kuma muna kokarin ganin hakan.
Tambaya: Me kuke yi wajen magance matsalar?
Amsa: Ba zan iya fada maku abin da muke yi ba a nan, hakan ba zai zama daidai ba. Amma muna kokarin cin ma wannan matsala.
Tambaya: Kace kana zargin wasu manya na da hannu cikin wannan rikici, bincike ne ya nuna maka hakan?
Amsa: Rikcin yana da alaka da wadannan mutane, kuma ba wai dukkanin su bane mutanen yankin. Akwai wasu dabam daga wasu bangarorin da ba na Neja-Delta ba. Suna wannan aiki ne ba don cigaban yankin ba ko kusa.
Tambaya: Me ya sanya wasu shuwagabannin yankin ba su son a tattauna da Gwamnati kan wannan batu?
Amsa: Ni, iyaka sani na, ban san wani Shugaba a yankin Neja-Delta da bay a son ayi zaman tattaunawa da Gwamnati ba.
KU KARANTA: ALHAJI ALIKO DANGOTE YAYI ALKAWARIN GINA ASIBITOCIN YOBE
Tambaya: Ina maganar cewa Shugaban Kasa ya fifita Bangaren san a Arewa bisa wasu?
Amsa: Idan mu ku duba abin da kyau, za a ga ba haka bane. Mu duba tun daga Shekarar 1999 har wa yau, za a fahimci haka. Sai dai mutane na son sukar duk wanda yake yaki da sata da barna a Kasa.
A karanta cikakkiyar hirar a shafin mu na Turanci.
The post Minista yayi bayani dangane da Nija Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.