Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Kasar Turkiyya

0

– Sojojin Kasar sun yi kokarin hanbarar da Shugaban Kasa Erdogan na Turkiyya.

–  Mutane fiye da 50 suka bakunci lahira dalilin hakan.

– An kubutar da Shugaban Hafsun sojin Kasar bayan da an kama sa.

– Gwamnatin Kasar karkashin Recep Tayyip Erdogan tace har yanzu tana da karfin iko

Wani bangare na Sojin Kasar Turkiyya sun yi kokarin yin juyin mulki a ranar 15 ga wannan watan. Bangaren da aka saka ma suna “Peace at home movement” sun yi kokarin hanbarar da Gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan. Jaridar Mirror ta bayyana cewa, ana ta jin karar harsashen bindiga ta ko ina a Babban Birnin Ankara, kuma jiragen soji na yawo a sararin samaniya, ga kuma manyan tankokin yaki bisa kan hanyoyin titi. An dai kafa dokar kulle, kuma an garkame kafar yanar gizo a Kasar. Kawo yanzu haka kowa na kulle a gida, sai ‘yan sanda da ke aiki a gari, abin dai kamar ana yaki! An rufe kan iyakokin kasar; Gadar Bosphorus ta Istanmul da Fatih Sultan Mehmet duk suna rufe.

KU KARANTA: DAN WASA YAYI MA MUTANEN KASAR FARANSA TAAZIYA

Shugaba Erdogon na Kasar ya kira magoya bayan sa da su hau bisa titi, sun yi zanga-zanga da nuna rashin yardarm su ga sojojin da ke koakrin kwace mulkin Kasar. Firayim-Ministan na Kasar Turkiyya, Binali Yildirim yace wadanda suka yi kokarin kifar da Gwamnati mai-ci cikin soji za su dandana kudar su. Yildirim yace ba za a bari wani abu ya kawo tasgaro ga tsarin damokaradiyyar Kasar ba. An kuma samu ceto Shugaban Hafsun Sojin Kasar, Hulusi Akar, bayan da an kama sa lokacin da ake yunkurin kifar da Gwamnatin Kasar. Wani babban jami’in na Turkiyya ya bayyana cewa sojojin sun so hambarar da mulkin Kasar ne cikin dare, ta hanyar tankokin yaki da jiragen sama.

Kasar dai ta bayyana an kama sojin Kasar har 1563 da ke da hannu cikin juyin mulkin. Kuma mutane sama da 60 suka rasa rayukan su, inji Jaridar Telegraph. Shugaba Erdogan na Kasar Turkiyya da yake magana a wajen filin jirgin saman Istanbul Ataturk yace ba za ta yiwu a kifar da Gwamnatin da jama’a suka zaba ba, ya kira jama’a da su tsaya tsayin-daka a Safiyar yau da yake jawabi.

 

The post Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Kasar Turkiyya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса