Siasia ya mika sunayen ‘yan wasan da za su buga Olympics
LABARIN WASANNI
Siasia ya mika sunayen ‘yan wasan da za su buga Olympics.
– ‘Yan wasa Mikel Obi da Akpeyi aka zaba cikin wadanda suka wuce Shekarun buga Gasar da za a kara a Birnin Rio na Brazil.
– Tauraron Chelsea, John Mikel Obi ne zai zama kyaftin din yan wasan.
– Za a fara fafatawa ne a Ranar 4 ga watan Agusta, inda Najeriya za ta kara da Japan.
Kocin Yan wasan kwallon Kafar Najeriya (Masu shekaru kasa da 23) ya mika sunan yan wasa 23 da za su kara a gasar Olympics na bana. Siasia Samson ya mika jerin sunayen yan wasan masu kasa da Shekaru 23 ga Hukumar Kwallon Kafar Kasar ta NFF. Za a fafata ne a garin Rio de Janeiro na Kasar Brazil.
A SAUKE MANHAJAR MU NA NAIJ.COM DOMIN SAMUN LABARIN WASANNI.
Dan wasan tsakiya na Chelsea, Mikel Obi da Dan wasan da ke tsaron gidar Chippa United, Daniel Akpeyi ne aka zaba a matsayin yan wasan da suka wuce shekaru 23 da su jagoranci Kasar a Gasar ta Olympics da za a buga a Brazil. Goal ta bayyana cewa wata Majiya mai karfi daga Hukumar NFF ta Kasar ta bayyana cewa Samson Siasia, mai horar da yan wasan na Najeriya ya dauki mutum 2 ne kacal da suka zarce shekaru 23, maimakon ukun da aka kayyade. Za dai a take wannan gasa wata mai zuwa a garin Brazil. Shi dai dan wasan tsakiyar nan mai tare na Chelsea, Mikel Obi ya sha nuna muradin sa na jagorantar Kasar a gasar, babu mamaki da Samson Siasia ya zabe sa, ya kyale sauran yan wasa irin su Ahmed Musa, Odion Ighalo da wasan su.
Kasar ta Najeriya dai ta samu nasarar cin gwal a gasar da aka buga a Shekarar 1996. Haka dai ta zo na biyu a Beijing da aka buga gasar Olympics din a shekara ta 2008. Kodayake Kasar ba ta samu zuwa gasar ba a shekarar 2012, ana sa ran za ta tabuka abin kirki a wannan karo. Yanzu haka dai, yan wasar Kasar na ta faman shirye-shirye a Kasar Amurka.
KU KARANTA: HUKUMAR FIFA ZA TA TAIMAKA MA NAJERIYA DA KUDI
The post Siasia ya mika sunayen ‘yan wasan da za su buga Olympics appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.