PMB ya umarci IGP da sake bude laifin kisar Bola Ige, Dokubo
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 17 ga watan Yuli, ya umarci Inspecto-Janar na yan sanda Ibrahim Idris da ya fara sabon bincike kan rikicin kisa da ba’a magance ba da Attorney-Janar na tarayya kuma ministan shari’a Chief Bola Ige da kuma tsohon mataimakin shugaban kudu maso kudu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) […]
The post PMB ya umarci IGP da sake bude laifin kisar Bola Ige, Dokubo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi 17 ga watan Yuli, ya umarci Inspecto-Janar na yan sanda Ibrahim Idris da ya fara sabon bincike kan rikicin kisa da ba’a magance ba da Attorney-Janar na tarayya kuma ministan shari’a Chief Bola Ige da kuma tsohon mataimakin shugaban kudu maso kudu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kasa, Chief Aminosari Dokubo, ya kuma fito da masu laifin da suka aikata kisan.
Mutuwar mushahuran mazaje biyu ya kasance keta doka a kasar, yayin da yan Najeriya suka yi kira ga gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ta nemo wadanda suka yi kisan wanda aka kasa gano wa har yanzu.
A tuna cewa, an harbe tsohon gwamnan jihar Oyo, Bola Ige har lahira a dakin sa da ke hanyar Bodija na garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo,da misalign karfe 9 na dare a ranar 23 ga watan Disamba, shekara ta 2001, bayan ya dawo Ibadan daga jihar Lagas da misalign 8.30 na dare.
An ce Masu tsaron da ke kula da tsohon ministan lantarki, sun nemi izinin daga Bola Ige kan zasuje cin abinci kafin a aikata kisan.
An bayyana cewa masu kisan sun jira a farfajiyar tsohon AGF sin kafin su samu shiga cikin gidan sa, suka kuma daure iyalansa. An rahoto cewa daya daga cikin masu harin ya nuna binga ga iyalansa ya kuma umarce shi da ya jagorance shi zuwa sama inda dakin tsohon gwamnan jihar Oyo yake.
KU KARANTA KUMA: Soyinka ya bukaci a kai barayin Najeriya gidan yari
An ce masu kisan sun tisa keyan matar marigajin da dansa zuwa wani daki inda ya kulle su kafin ya harbi Bola Ige a kirjinsa.
Vanguard ta bayyana cewa domin gano makarkashiyar kisan, Inspecto-Janar din yan sanda Ibrahim Idris ya kafa wata tawagar bincike wanda ke karkashin kulawar mataimakinsa , domin gano bakin zaren lamarin.
A bangaren kisan shugaban PDP, an kasha shine a yayin da yake dawowa gidansa daga Abuja bayan wani taro masu kisan sun mamayeshi ne a lokacin da ya kusa shiga jihar Delta.
An kasha Dokubo a kusa da Asaba a ranar 22 ga watan Octoba na shekara ta 2014.
The post PMB ya umarci IGP da sake bude laifin kisar Bola Ige, Dokubo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.