Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

Tsagerun Neja Delta sun ba shugaba Buhari uzurin karshe

0

Daya daga cikin tsagerun nan na Neja Delta masu tada kayar baya watau Niger Delta Justice Defense Group (NDJDG) sun fitar da wata sanarwa suna mai ba shugaba Buhari uzurin karshe a cewar su.

Niger Delta Avengers

Tsagerun sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da suka fitar da kuma NAIJ.com suka samu suna mai cewa shugaba Buharin dole ne ya saurari bukatun su ko kuma su kaddamar da wani gagarumin hari cikin satukan dake tafe. Shugaban kungiyar tsagerun ta NDJDG ya ce: “Mu muka dauki alhakin kai har a kan bututun man B-dere dake karamar hukumar Gokana jihar Ribas ranar Asabar din da ta gabata 16 ga watan Juli na 2016.

“Wannan daya ne kacan daga cikin shire-shiren mu na hare-hare da zamu kaddamar idan har ba’a biya mana bukatun mu ba cikin satittukan nan masu zuwa. Su dai tsagerun na NDJDG a baya sun dauki alhakin kaddamar da hare-hare akan bututun mai a karamar hukumar Tai dake jihar ta Ribas.

A baya dai tsagerun sun zayyana wasu bukatun su guda 4 da suka aike da su zuwa ga gwamnatin tarrayya. A cikin mukatun kuma sun hada da samun yancin gashin kai tare da damar mallakar man fetur din dake yanken nasu tare kuma da tunawa da dukkan wadanda suka mutu wajen fafutukar nemar ma yankin yanci da dai sauran su.

The post Tsagerun Neja Delta sun ba shugaba Buhari uzurin karshe appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса