Dogara nada hannu cikin canje-canjen kasafin kudin 2016
–Hujjan cewa kakakin majalisan wakilai ta kasa, Yakubu Dogara ,na da hannu cikin rufa rufan kasafin kudin 2016 ta fito
–Akwai kuma hujjan cewa yakubu dogara ya gayyace yan majalisu zuwa gidanshi domin daukan rantsuwa.
Abdulmumin Jibrin
Game da wata binciken da Jaridar Sahara Reporters ta gudanar, kakakin majalisan wakilan tarayya, Hon. Yakubu Dogara , tare da wasu shugabannin majalisan 3 na da hannu a cikin canje-canje da akayi cikin kasafin kudin tarayya ta shekaran 2016
Jaridar Sahara Reporters ta kawo hujja akan wannan , wanda yake kara karfafa zargin da tsohon shugaban kwatimitin kasafin kudi,Hon Abdulmumini Jibrin ,yayi na cewa kakakin majalisan wakilan tarayya, Yakubu Dogara, na da kasha a gindi.
Kakaki Yakubu Dogara
Bayan haka ma, akwai rahoton cewa Yakubu Dogara da kawance da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Osun,kuma dan takaran gwamnan Jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore. An kuma tuhumci kakakin majalisan wakilan tarayyan da kai yan majalisu gidansa domin daukan rantsuwa.
Ku tuna cewan kwanan nan Mr. Abdul Mumini Jibrin yayi maganan cewan Mr. Yakubu Dogara na yunkurin bata mai suna kuma yana amfani da ‘yan sanda domin cin mutuncin sa , bibiyan sa da kuma tsoratar da shi.
KU KURANTA : Mutane 9 sun raunana yayinda yan daba suka far ma majalisa
Hakazalika, kakakin majalisan wakilan tarayya, Mr.Yakubu Dogara ya mayar da martani akan hakan. Shi ma ya bada labarin abinda ya faru kuma yan mamakin dalilin da yasa Abdulmumini Jibrin bai fito yayi maganan ba sai yanzu.
The post Dogara nada hannu cikin canje-canjen kasafin kudin 2016 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.