Mun ba Buhari makonni 3 – ‘Yan bindiga
– ‘Yan bindigan Neja Delta sun basu yarda da cewan kungiyar tsiratar da neja delta watau MEND ta wakilce su wajen tattaunawa da gwamnatin tarayya ba akan hayaniyar da ke faruwa a yankin
–Kungiyoyin sun nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito da jerin sunayen wakilan gwamnatin tarayya cikin makonni 3.
yan kungiyanmend
Yan bindigan yankin Neja Delta sun ki amincewa da Kungiyar Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND)a matsayin shugaban tawagar wakilan yan bindigan Neja Delta a tattaunnawan sulhun da za’ayi da gwamnatin tarayya.
Daga cikin kungiyoyin da suka ki amincewa da shugabancin MEND sune Ultimate Warriors da Niger Delta Revolutionary Crusaders (NDRC) wanda suka ce kungiyar bata da hurumin yin Magana da yawun yan bindigan neja delta saboda ta kasance tana goyon bayan gwamnatin tarayya akan yankin Neja Delta.
A wata jawabin da aka aika ma Jaridar Vanguard, kungiyoyin sun baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari mako 3 ya fito da jerin sunayen tawagar wakilan gwamnatin tarayya. Sun jaddada cewa tawagar ta kunshi yan kasar waje saboda ta daina kai hare-haren kafufuwan man fetur a yankin.
Hakazalika, Kungiyar Niger Delta Avengers (NDA) na zargin wasu jami’an tsaro da hadaka da kungiyar MEND da wasu mayaudara wajen sanyan bam a wasu bututun mai domin kama wasu mutane maras alhaki da sunan kama ‘yan ta’adda saboda shugaban kasa ya dauka suna kokari.
Ku tuna cewam kungiyar ta lashi takobin durkusar da tattalin arzikin kasa.
KU KARANTA : Tsagerun Neja Delta sun ba shugaba Buhari uzurin karshe
Mambobin kungiyar MEND sune
Mr. Henry Odein Ajumogobia, SAN ( shugaban tawagar)
HRH King Alfred Papapreye Diette-Spiff, Amayanabo of Twon-Brass (Bayelsa state) as mataimakin shugaban kuma wakilin Niger Delta Dialogue and Contact Group – NDDCG).
– Senator Florence Ita-Giwa (Cross River) mai wakiltar yan bindigan Bakassi axis,
– Mr. Ledum Mitee, Esq.( Rivers state)
– Senator Adolphus Wabara
– High Chief Government Ekpemupolo, alias Tompolo, (jihar Delta ),
– Mr Ibanga Isine (Jihar Akwa Ibom),
– Mr. Alfred Isename (jihar Edo),
– Mr Timipa Jenkins Okponipere, Esq. (Bayelsa )
The post Mun ba Buhari makonni 3 – ‘Yan bindiga appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.