Shugaba Buhari yayi Tir da harin Munich
– Kasar Najeriya shirye ta ke da ta taimaki Kasar Jamus da Nahiyar Turai baki daya wajen fada da ta’addanci.
– Shugaba Buhari na Najeriya yayi Tir da harin da aka kai a Kasar Jamus ta tsakiyar Turai.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nuna matukar takaicin sa da alhini dangane da harin da aka kai a Birnin Munich na Jamus. Wani matsahi kurum ya shiga buda wuta a babban Birnin inda yayi sandaiyyar aikawa da mutane 9 har lahira, ya kuma raunata mutane kusan 27. Mai taimakawa Shugaban Kasar kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina ya bada wannan jawabi. Shugaba Buharin yana cewa: “A daukakin Jama’ar Kasar Tarayyar Najeriya, Shugaba Buhari na mika ta’aziyyar sa ga iyalan da abin ya rutsa da su wajen wannan mummunan aiki”
KU KARANTA: JUYIN MULIN KASAR TURKIYYA: AN KAMA MUTANE FIYE DA 10,000
Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yace abin takaici ne ace ana kai irin wannan munanan hare-hare maras ko dadin ji a fadin duniya ga wadanda ba su ji ba, ba su kuma gani ba. Shugaban Kasar na Najeriya, Buhari yace Kasar sa da mutanen san a tare da ‘yan Kasar Jamus a cikin wannan hali, kuma za ta (Kasar Najeriya) ta yi iyaka kokarin ta wajen taimakawa Kasar Jamus ganin bayan ‘yan ta’adda a irin wannan yanayi.
KU KARANTA: JUYIN MULKIN KASAR TURKIYYA: AN KAMA MUTANE FIYE DA 10,000
Wannan ne dai hari na uku da aka kai a cikin yammacin Turai cikin kusan mako guda. Ana dai kai harin ne ga mutanen farar hula, wanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. An kai sauran harin ne a Kasar Faransa da kuma Jamus din a baya. Duk Kungiyar ISIL ta dauki nauyin na bayan.
The post Shugaba Buhari yayi Tir da harin Munich appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.