Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Июль
2016

An gano Sojojin da suka bata wajen fada da Boko Haram

0

– A wani harin kwantan-bauna da Yan Boko Haram suka kai Sojojin Najeriya a Ranar 20 ga wannan watan, Sojoji 19 ne suka raunata bayan haka kuma aka nemi wasu aka rasa.

– Abin farin cikin shine cewa, Rundunar Sojin Kasar ta bayyana cewa an gani Sojojin da suka batan a wannan hari.

 

 

 

 

 

 

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa, an gano Sojojin da suka bata a wajen fada da Yan Boko Haram a Jihar Borno da ke Arewa-maso-gabashin Kasar. An dai bayyana cewa an rasa inda Sojojin suka shiga a baya. Sojojin na Najeriya sun bace ne bayan wani hari na kwantan-bauna da yan ta’addan na Boko Haram suka kai masu a garin Guro Gongon a ranar 20 ga wannan watan na Yuli, 2016, a cewar Rundunar Sojin Kasar ta Najeriya.

Abin murnar shine cewa, yanzu haka an samu gano wadannan Sojoji da a baya da aka nema aka rasa. Mai magana da yawun Sojin na Najeriya, Kanal Sani Kukasheka Usman ya bayyana cewa an samu gano Sojojin da suka batan. An dai gano Sojojin nan ne bayan an tsananta bincike da kokarin ganin an ceto su. An yi amfani da kayan aikin sama da kuma wata rundunar musamman da tayi ta kokarin sintiri. Kanal Kukasheka Usman ya sanar da jama’a cewa, bayan an zafafa bincike, an gano Sojojin Kasar da suka bata a baya a safiyar jiya. Sojojin dai manyan jami’ai ne har su 5, ciki akwai mai ba rundunar umarni. Duk da dai cewa suna cikin koshin lafiya, an dai kai su asibitin Rundunar, cewar Kanal Kukasheka.

KU KARANTA: JUYIN MULIN TURKIYYA: AN KAMA MUTANE FIYE DA 10, 000

A baya dai Kanal Kukasheka ya bayyana yadda Sojojin suka bace, da kuma yadda aka kashe yan ta’addan na Boko Haram da dama a harin. Sojojin dai kuma sun gano wasu makamai daga wajen ‘yan ta’addan na Boko Haram a Garin Guro Gongon na Borno.

 

The post An gano Sojojin da suka bata wajen fada da Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса