Zaben Jihar Ondo: Jam’iyyar SDP tayi korafi
–Jam’yyar SDP ta kawo kuka akan zaben neman kujeran gwamnan da za’a gudanar a Jihar Ondo
–Jam’iyyar tace ana kulle kullen shirin daure shugaban jam’-yyar ta kasa,Cif Olu Falae.
–Cif Olu Falae na daga cikin yan siyasan da suka dibi sanwa daga tukunyar badakalar kudin makamai wanda aka fi sani da #DasukiGate
Olu Falae
A jiya ne , 21 ga watan yuli, jam’iyyar SDP ta fara korafin cewa ana shirin daure shugaban jam’iyyar ta kasa ,Cif Olu Falae akan zaben neman gujeran gwamnan da za’a gabatar a jihar Ondo.
Kakakin jam’iyyar ,Alhaji Alfa Mohammed, ya bayyana ma manema labarai cewan akwai yan siyasan adawa da basu son Cif Olu Falae ya kasance a cikin al’umma lokacin zaben da za’a gudanar a ranar 23 ga watan nuwamba saboda fada a jin da yake da shi.
Game da Alfa Mohammed, ana son akama falae saboda kudi N100 miliyan da jam’iyyar SDP ta karba daga hannun jam’iyyar PDP kafin zaben 2015. Ya fada ma manema labarai cewa jam’iyyar SDP ta shiga wata kawance da jam’iyyar PDP kafin zabe, wanda kuma irin wannan kawance sanannan abune a siyasa. Ya kuma musanta zancen cewa Cif Olu Falae ya amsa kudin dan amfanin kansa da sunan jam’iyya. ” Ba Falae kacokal ne ya shiga kawance da jam’iyyar PDP ba ,jam’iyya ce. Jam’iyyar SDP ne ta shiga yarjejeniya da PDP lokacin zaben neman kujeran shugaban kasa, wanda kuma irin wannan kawance sanannan abune a siyasa.”Mohammed ya fada.
KU KARANTA : Bode George Ya Roki PDP Ta Zabi Mutum Mai Nagarta
A farkon shekaran nan , Falae ya fada ma shugabannin jam’iyyar SDP a wato ganawa a Abuja cewa abun kunya ne a gareshi an dinga jingina shi kudin badakalar makamai $2.1biliyan. Falae yace zai fili akan kudin N100milyan daya karba a hannun tsohon shugaban mashawartar amuntattun jam’iyyar PDP, Cif Tony Anenih.
A lokacin , jama’an cocin da falae ke zuwa bauta , -St. David’s Cathedral, Ijomu street da ke birnin Akure , sun yi masa gudan abin kunya na fitowan sunan shi a cikin Wadanda suka lashi badakalar kudin makamai.
The post Zaben Jihar Ondo: Jam’iyyar SDP tayi korafi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.