Kudirin mu na tsabtace Najeriya-Ministar Muhalli
Kudirin mu na tsabtace Najeriya da kuma samar da aiki ga jama’a-Ministar Muhalli
NAIJ.com tayi hira da Ministar Muhalli ta Najeriya, Misis Amina Mohammed a ofishin ta da ke Abuja. Ta bayyanawa Aderonke Bello na NAIJ.com tarihin rayuwar ta, karatun ta, da kuma harkar shugabanci, musamman mata. Ministar tayi magana dangane da harkar ofishin ta, manufofin ta, da kuma ayyukan da suke yi. Karanta wannan hirar ta su nan kasa:
NAIJ.com: Ya labarin karatun ki?
Na fara karatu na ne a Kaduna, daga nan na wuce Birtaniya domin cigaba, bayan nan, na dawo Najeriya a shekarar 1980. Nan nayi wasu ayyuka, daga nan kuma na hadu da wasu yan kwangila, inda na yi shekara goma sha daya muna aikin kwangila a bangaren da ya shafi kiwon lafiya, makarantu da sauran su dai a Arewacin Kasar nan. Daga nan ne Shugaba Obasanjo ya kira ni, Ministan Ilmi na wancan lokaci ya bani wani aiki, bayan shekara 4 na kammala. Bayan nan ne na zama mai bada shawara ga harkar MDG. A MDG ne muka yi gagaruman ayyuka, na tsawon shekaru 7. Haka kuma na karantar a Jami’ar ‘Columbia’ da ke Birnin New York, bayan nayi karatun digirgir a fannin cigaba da siyasa.
NAIJ.com: Ko ke asalin mutumiyar in ace?
Uba na, mutumin Kasar Gombe be. Uwa ta kuma Baturiyar Birtaniya ce.
KU KARANTA: SOJIN NAJERIYA SUN FATATTAKI YAN BOKO HARAM
NAIJ.com: Ya huldar ki da sauran abokan aikin ki, Ministoci, ganin ki na mace?
Sauran Ministocin abokai ne ne, da yanuwa, saboda haka ba za su muzguna mani ba do ina mace. Kuma duk kwararru ne, suna kokarin taimakawa wajen gyara tattalin Kasa da al’umma. Ina karuwa da ilmin su kwarai da gaske. Kuma Shugaban Kasa ya bayyana kudurin sa, wanda ya zama dole mu hada hannu da karfe wajen ci ma hakan. Shugaban Kasa ya yarda da mu, ya kuma yadda da kwarewar mu, ba za mu basa kunya ba.
Za a iya karanta cikakkiyar hirar a shafin mu na Turanci.
The post Kudirin mu na tsabtace Najeriya-Ministar Muhalli appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.