Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

EFCC ta kai farmaki ofishin filin jirgin sama a Legas

0

–Hukumar hana Almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta gudanar da wata farmakin bincike ofishin ajiye kayayyakin jirgin sama watau National Aviation Handling Company NAHCO da ke babban filin jirgin sama Murtala Muhammed a Jihar Legas.

–Wata majiya a rahoton tace mana daga cikin ma’aikatan da aka bincika sune sakataren kamfanin, shugaban bangaren duban tasarrufin ciki da wasu manyan ma’akatan kamfanin.

Hukumar yaki da rashawa masu tashe watau hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kai farmakin bincike ofishin ajiye kayayyakin jirgin sama watau National Aviation Handling Company NAHCO da ke babban filin jirgin sama Murtala Muhammed a Jihar Legas.

Game da Jaridar Punch, an gudanar da binciken ne ranan alhamis dinda ya gabata na misalin awa 3, yayinda jami’an Hukumar EFCC ta gudanar da bincike mai zurfi akan na’urar komfutan su da kuma ofishin dubin tasarufi.

Wata majiya a rahoton tace mana daga cikin ma’aikatan da aka bincika sune sakataren kamfanin, shugaban bangaren duban tasarrufin ciki da wasu manyan ma’akatan kamfanin. Ta kara da cewa ana kyautata zaton anyi binciken ne bayan Koran manyan ma’aikatan wurin da akayi a ranar litinin da ya gabata

“Sun binciki sakataren kamfanin, da shugaban ma’akatan akawu da tattalin arziki, da ayyukan amfani,da kayan jirgi kuma basu bar wurin ba har misalign karfe 8 na dare,

KU KARANTA : Rashawa:Buhari zai kore ne in ina da laifi – Amaechi

Kuma shugaban sadarwa da ayyukan kamfanin NAHCO ,Mr Tayo Ajakaye wanda ya tabbatar da kawo binciken ya bayyana a wata jawabi cewa akawun kamfanin, Bamidele Adelaja ya bada hadin kai ga jami’an EFCC

“Yayinda basu samu manyan kamfanin guda 2 ba, Jami’an  EFCC suka nemi ganin akawun kamfanin, Mr. Bamidele Adelaja,wanda suka kasance tare dashi yana musu bayanai aka wasu takardun da suke bukatan gani. Akawun ya tabbatar da cewa ma’aikatan hukumar EFCC sun nuna masa takardan izinin gudanar da bincike,kuma yace kamfanin NAHCO na shirye ta bada hadin kai da jami’an gwamnati a koda yaushe kuma zamu aiwatr da hakan yanzu. Sun kawo ziyaran binciken ne misalin karfe 4pm kuma sun gama misalign karfe 7pm, kuma sun tafi da wasu.

The post EFCC ta kai farmaki ofishin filin jirgin sama a Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса