Gwamnatin Jihar Kebbi na sa hannun jari a Ilimi da aikin noma
–Daliban Makarantun Jihar Kebbi na karatu a ajujuwa marasa kujeru
–An dauki hoton gwamnan zaune a kasa da wasu dalibai
–A yanzu haka, gwamanati ta samar da kujeru
Gwamnatin Jihar Kebbi ta fara raba kujeru da wasu kayayyakin aji ga duka makarantun firamare da sakandare da ke fadin Jihar.
A farin shekaran nan, an samu wani hoton gwamnan jihar ,Abubakar Atiku Bagudu, zaune a kasa da dalibai guda biyu, wannan hoton ya yadu a kasa. A lokacin, gwamnan ya sha suka daga bakin mutane na kokarinsu sa siyasa a abun maimakon kawo gyara.
Amma, a wata jawabin da babban mai baiwa gwaman shawara akan labarai, Aisha Augie-Kuta, gwamanan da mukarrabansa sun kai ziyara kimanin makarantu 170 da ke fadin jihar tun lokacin da hau ragamar mulki kuma ya alanta kalubalen da makarantun ke fuskanta wanda ya kunshi lalacen gine-ginen makarantun, rashin kujeru da tebura da kuma yawan malamai wadanda basu cancanta ba da su koyar ba,wanda ya sa ba’a kawo yara kuma suna fadi jarabawa.
KU KARANTA : Ogbeh yayi magana dangane halin da ‘Yan Najeriya ke ciki
“Gwamanatin jhar ta alanta bangaren ilimi da wasu shirye-shirye na jawo hankali iyaye akan muhimmancin ilimi, gyara ginin makarantu, samar da kujeru da tebura, horar da malamai da kuma gina su yanada zasuyi kafada da kafada da abubuwan d ake bukata a bangaren ilimi.”
Ta kara da cewa wannan na bisa gwamnatin canji ne da kuma fadada aikin noma, Jihar Kebbi ta samo kayan aiki domin noman zamani saboda bunkasa girben amfanin noma a Jihar.
“Haruna Abubakar, Shugaban ma’aikatan aikin noma ya mika kayayyakin noma domin kaisu jihar kebbi, Mrs. Augie-Kuta ta fada a wani jawabi cewa “an yi biki mika kayayyakin aikin ne a cibiyar gudanar da bincike akan ayyukan noma,da ke mabushi a Abuja a ranan juma’a,22ga watan yuli.”
The post Gwamnatin Jihar Kebbi na sa hannun jari a Ilimi da aikin noma appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.