Shari’a na da EFCC bazai dameni ba- Dokpesi
–Raymond Dokpesi ya bayyana cewa chajin cin hanci da rashawa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato (Economic and Financial Crimes Commission, EFCC) keyi a kanshi bazai shafi yunkurinshi na son zama shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba
-Dokpesi yace gwamnatin tarayya ko jam’iyyar All Progressives Congress (APC), bazasu iya amfani da chajin su yaudare shi ba idan aka zabe shi
Raymend Dopkesi
Raymond Dokpesi ya bayyana cewa chajin cin hanci da rashawa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi a kansa ba zai shafi yunkurin san a zama shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba,ya bayyana cewa bai san komai ba a kai har sai kotu ta bayyana shi a matsayin mai laifi.
KU KARANTA KUMA: Kwankwaso na shirya makircin rushe zaben da za’ayi- KNSG
Ya ce gwamnatin Tarayya ko jam’iyyar All Progressives Congress (APC) baza su iya amfani da chajin a matsayin karkuwa ba idan aka zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar adawa, PDP. Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi lokacin gamuwar sa tare da wakilai daga jihar Kwara, a sakatariyar jam’iyyar a garin Ilorin.
A kan Sheriff yace gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki suna namen shi domin sulhu da zaman lafiya. Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kwara, Barrista Akogun Oyedepo, ya yabe shi kuma ya tabbatar mai da samun goyan bayansa, tare da cewa ya kafa wani misali dan wasu su bi.
The post Shari’a na da EFCC bazai dameni ba- Dokpesi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.