An kama yan Kurkuku 6 da suka gudu
–An kama 6 daga cikin yan kurkuku 13 da suka arce daga kurkukun Koton-Karfe da ke Jihar Kogi
–Kwantrola Janar da gidajen yari, Ja’afaru Ahmed yace a kamasu su tare da sa hannun wasu jami’an tsaro .
–Yace ya shirya wata kwamiti domin gudanar da bincike gamsashe akan balle kurkukun da akayi.
An kama 6 daga cikin yan kurkuku 13 da suka arce daga kurkukun Koton-Karfe da ke Jihar Kogi. Game da Jaridar Punch, Ja’afaru Ahmed, kwantrola janar na gidajen yarin, ya bayyana cewa an kama 6 daga cikinsu tare sa hannun wasu jami’an tsaro da kungiyoyin yan banga, yace an dawo da su gidan yarin.
Ahmed, wanda ya ziyarci kurkukun koton karfen ya tabbatar da cewa yan kurkuku 13 sun gudu a ranar asabar ,30 ga watan yuli. Wanda ya kunshi masu jiran gurfana 10 da kuma masu tabataccen laifi 3, game da jawabin da kakakin jami’an Kurkuku ,Francis Enobore ya fada.
Kwantrolan hukumar yace ya shirya wata kwamiti ta musamman domin gudanar da bincike mai zurfi akan abubuwan da suka faru har yan kuruku suka arce kuma suka kawo sakamakon binciken domin daukan mataki .Yana bada wanna tabbacin cewa za’a dau mataki akan yadda za’a rage cinkoson da ke cikin gidajen yarin , musamman masu jiran gurfana a bisa ga canjin gwamnatin tarayya keyi.
KU KARANTA : Indonesia ta zartar da hukuncin kisa kan ‘yan Nigeria
Ahmad ya kara da cewa an shirya aikin tsaro domin karafa ciki da wajen gidajen yari da ke fadin kasan gaba daya domin kiyaye gaba. Wannan shine karo na 3 na balle kurkuku a gidan yarin koton karfe tsakanin shekaran 2010 zuwa 2013.
A bangare guda, an kama wata jami’ar hukumar gidajen yari bayan a kama ta tana shigo da kayan maye zuwaga yan kurkuku a kirikiri. Jami’ar ta musanta wannan zargin cewa bata yi ba.
The post An kama yan Kurkuku 6 da suka gudu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.