Bazaka iya cire Ekweremadu ba, matasan Igbo
-Kungiyar Inyamurai na Ohanaeze Ndigbo Youth Council sun gargadi gwamnatin tarayya da ta daina makircin cewa zata cire mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu
-Matasan Ohanaeze sunce yan Kudu maso Gabas suna jin dadin Sanata Ekweremadu da nasarorinsa a majalisar Dattawa
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu
Wani kungiyar matasa na Ohanaeze Ndigbo Youth Council sun gargadin gwamnati mai cin a karkashin jam’iyyar APC da ta daina makircinta na cire mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, cewa yan Najeriya zasuyi zanga-zanga kan ko wani yunkuri na cire Ekweremadu daga Ofishin sa.
A cewar kungiyar, “Yan Najeriya daga ko wani bangare suna jin dadin shugabancin yan Majalisar Dattawa, don haka wadanda ke shirya makircin barazana ga shugaban majalisar mussaman Ofishin mataimakin shugaban majalisar wanda ke karkashin Sanata Ike Ekweremadu, su daina wannan yunkurin domin bazasu samu nasara ba.”
KU KARANTA KUMA: Kotu ta bada umarnin kama shugaban APC
A wata sanarwa daga Hon. Obasi Ogbonnaya, mai kula da kungiyar Ohanaeze Youth yankin Arewa yace “ yan kudu maso gabas na jin dadin Sanata Ekweremadu da nasarorinsa a majalisar Dattawa.”
“Yan mazabarsa a gabashin Enugu da yan kudu maso gabas gaba daya suna jin tasirin sa a majalisar. “mun samu labarin cewa wasu yan hana ruwa gudu daga jam’iyyar APC na kudu maso gabas suna neman mambobin majalisar dattawa da shugaban kasa da sub a da goyon bayansu ga mugun nufinsu na barazana ga odishin shugaban majalisar dattawa. Muna gargadin irin wadannan da su daina irin wannan yunkurin domin baza suyi nasara ba.
The post Bazaka iya cire Ekweremadu ba, matasan Igbo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.