Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Wani mutumin kasar Sin ya kashe kansa a jihar Lagas

0

-Yan sandan jihar Lagas sun gano gawar wani mutumin kasar Sin a dakin sa a ranar Alhamis 28 ga watan Yuli

-An rahoto cewa mutumin kasar Sin din ne ya kashe kansa

-Har yanzu ana binciken yanda kisar ta afku a cewar kakakin yan sandar jihar Lagas

Dolapo Badmos

Ranar Alhamis 28 ga watan Yuli ya kasance bakon rana ga yan sanda dake Ikeja a jihar Lagas.

Jami’an yan sandan jihar Lagas sun gano gawar wani mutumin kasar Sin a dakin sa a lamba 11, Itohan Avenue, Ikeja.

Bisa ga jaridar Today, ana zargin dan kasar Sin din Si Guical mai shekaru 50 a duniya da kashe kansa.

An rahoto cewa ya rataye kansa a cikin dakinsa dake Ikeja. Ya rataye wuyansa kan wani karfe dake jikin tagar sa a dakin. Kakakin yan sandan jihar Lagas, Dolapo Badmos ce ta tabbatar da haka.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya saki matarsa saboda abinci

A cewar Badmos, masu bincike daga babban cibiyar yan sanda sun ziyarci gidan domin yin bincike. Ta ce an kai gawan Guical dakin ajiyar gawa domin gano abunda ya haddasa mutuwar.

A kwanan nan, aka kama wani mutumin kasar Sin mai suna Zhao Chun, da laifin shigo da sinadarai marasa rijista da ake amfani dasu gurin sarrafa bam kasar Najeriya.

An kama shi ne tare da abokin rakiyarsa dan Najeriya, mai suna Christian Ohia. A cewar jaridar Daily Post, Chum wanda ke da shekaru 33 a duniya, yana da Kamfanin kayan alatu a jihar Ogun. Jami’an National Agency for Food, Drug Administration and Control (NAFDAC) sun cafke shi ne a ranar Alhamis 21 ga watan Yuli.

The post Wani mutumin kasar Sin ya kashe kansa a jihar Lagas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса