Jibrin zai kai karan Dogara hukuma
Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisan wakilai ta kasa ,abdulmumini jibrin zai kai karan kakakin majalisa hukumomin yaki da rashawa da yan sanda. Jibrin ya bayyana hakan ne a safiyar yau ,litinin, 1 ga watan agusta cewa zai kai karan dogara hukumomi 4 yau .
“Za mu je Hukumar ICPC karfe 10, DSS karfe 12, EFCC karfe 2, da kuma hedkwatan yan sanda da katfe 4. Hukuma zata garkame algungumin kakaki dogara da sauran.” Jubrin yace.
kakaki Yakubu Dogara da Abdulmumin Jibrin
Amma, a karfe 11.09 na safe , Jaridar Naij.com na ICPC kuma jibrin bai garzayo ba . Wata majiya dake kusa da jibrin ya bayyana cewa tsohon shugaban kwamitin kasafin na tattara karan shine har yanzu. Yace jibrin da lauyoyin shi zasu garzaya hukumomin idan takardun suka cika.
Hayaniyar da ke faruwa tsakanin jibrin da kakakin majalisa Yakubu Dogara akan rufa rufan kasfin kudin kasa. Jibrin yace Dogara da wasu shugabannin sunyi kari cikin kasafin kudin kasa kimanin kudi N40 biliyan don aljihun kansu.
Jibrin na wannan tuhuman ne makonni 2 bayan kakakin majalisan ya cire shi a matsayin shugaban kwamiti. Tunda ya fara tuhumar, jibrin ya cigaba da hayaniya da wasu yan majalisan wakilai. Amma, ya bayyana cewa ya amince cewan yayi jinkiri wajen bayyana wannan babakeren cutan kasafin kudin.
KU KARANTA : Ya kamata EFCC ta kama Dogara –Jibrin Kofa
Jibrin ,yayinda ya ke magana akan wata hira da ya gabatar a shirin sunday politics a tashan yada labarai ta channels, yace duk da cewa yayi jinkirin fitowa da irin wannan maganan, amma a matsayin sa na shugaban kwamiti, bai kamata ya fito yayi magana akan abin.
The post Jibrin zai kai karan Dogara hukuma appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.