Ya zama dole Pogba ya zo Man Utd -Wayne Rooney
Jagoran yan wasan kungiyar kwallon kafa na Manchester United Wayne Rooney yace shi da Paul Pogba suna da abubuwan yi tare a kungiyar ta Man Utd a dai dai lokacin da kungiyar take kara zafafa neman da take yi wa dan wasan don ganin ta siye shi daga kungiyar sa ta Juventus.
Paul Pogba
Rooney ya shaida wa kamafin jaridar Daily Mail cewar har yanzu yana da raunukan da Pogba din ya ji masa a wajen atisaye tun shekarun baya sadda yana kungiyar. Da aka tambayi Rooney din abun da yake kewa game da Pogba din sai yace: “Ciwukan da yake ji mana. Pogba wani irin dan wasa ne da yake son ji wa mutane ciwo a lokacin atisaye”.
Idan dai har kuka yi atisaye tare to kam sai ya dan taba ka. Ko a hannu ko a kafa. Ba kuma lalle yana yin hakan ne ba a cikin sani amma dai kawai sai ka ga hakan ta faru.” Pogba dan wasa mai shekaru 23 yanzu ya bar kungiyar Man Utd ne shekaru 4 da suka wuce inda ya koma Juventus.
Yanzu haka dai sabon mai horar da kungiyar Mourinho ya sa ma dan wasan kahon zuka wajen ganin ya siye shi ko ta wane hali. Wannan ne ma yanzu haka ake cikin yin cinikin dan wasan a kan kudi €120m. Ana sa ran kuma a kammala cinikin dan wasan cikin kwanakin nan masu zuwa.
The post Ya zama dole Pogba ya zo Man Utd -Wayne Rooney appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.