Oxlade-Chamberlain ya ci wa Arsenal wata kayatattar kwallo
Sabbin yan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta siyo Rob Holding and Granit Xhaka sun zura kwallayen su na farko a kungiyar a wani wasa da suka buga da kungiyar Chivas dake kasar Mexico. Wasan dai ya tashi inda Arsenal ta lallasa Chivas din da 3 – 1.
Sabbin yan wasan dai na kungiyar Holding da kuma Xhaka an fara wasan ne da su tun daga farko. A wasan ne kuma Oxlade-Chamberlain ya zura cikon kwallon ta uku a wani yana yi mai kayatarwa.
Dan wasan na kasar Ingila duk da rashin kwazon da ya nuna a kakar wasan da ta gabata ya zura kwallon ne a jiya bayan ya jawo ta daga gida sannan kuma yayi tafiya mai tsawo kafin daga bisani ya zura kwallon shi kadai ba da taimakon wani dan wasa ba.
Zaku iya kallon kwallayen da aka ci a nan kasa:
Chuba Akpom vs @Chivas(2016). pic.twitter.com/L5Sj6D4hM1
— ArsenalGoals (@ArsenalGoaIs) August 1, 2016
Alex Oxlade-Chamberlain vs @Chivas(2016). pic.twitter.com/AywPRCLwsj
— ArsenalGoals (@ArsenalGoaIs) August 1, 2016
Rob Holding vs @Chivas(2016). pic.twitter.com/jnzEUWyD3h
— ArsenalGoals (@ArsenalGoaIs) August 1, 2016
The post Oxlade-Chamberlain ya ci wa Arsenal wata kayatattar kwallo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.