Abin mamaki, El-Rufa’i a coci
Gwamna Nasir El-Rufai ya kai wa amininsa Fasto Tunde Bakare a cocinsa don ya yi wa Najeriya Addu’a.
Cocin ta sanar da ziyarar gwamnan ne ta hanyar kafar sadarwa ta twitter. Gwamna El-Rufa’i wanda yake Musulmi ya gabatar ma majalisar jihar Kaduna wani kudirin doka mai cike da tirka tirka na tantance wa’azi. Kudirin dokan na nufin tantacewa da iyakanta yadda malamai zasu rika yin wa’azi a jihar, inda aka samar da hanyoyin hukunta duk wanda ya karya dokar. Watanni da dama tun bayan gabatar da kudirin dokar, cece kuce yaki karewa. Ganin El-Rufa’i da aka yi a coci ya janyo cece kuce a tsakanin jama’an Najeriya, inda wasu ke ganin cewa takarar shugaban kasa yake son yi a 2019.
The post Abin mamaki, El-Rufa’i a coci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.