An bayyana Lionel Messi amatsayin dan wasanna musamman
-Pope Francis ya lura Messi yafi Maradona da Pele.
-Shugaban chochin ta katolika ya fadawa mahalarta taron Ranar matasa ta Duniya.
-Pope Francis sanannan magoyin bayan Lorenzo ne.
Pele
Shugaban chochin katolika kuma magoyi bayan Lorenzo, Pope Francise ya bayyana cewa zakaran Barcelona wato Lionel Messi shine dan kwallon da ba’a taba yiba a duniya. A cewar shugaban chochin katolika din, dan wasan dai yayi nasaran samun lashe Ballon d’or har sau biyar don haka kuwa yafi sauran yan uwansa yan Argentina da Brazil wato, Diego Maradona da Pele.
Andai ta hada Messi da shahararrun da akai a baya musamman irin su, Maradona da Pele, kai harma da abokan wasan sa na yanzu musamman abokin hamaiyar sa dake kungiyar kwalo na Real Madrid wato Cristiano Ronaldo.
KU KARANTA : Nnamdi Kanu ya dauki nauyin gasar kwallon kafa
Pope Francis ya dai bayyana maganar shine a taron ranar matasa na Duniya, inda ya fadama Maza da Mata cewar ” ni a wurina {Lionel Messi} yafi Maradona da Pele. Messi ya sanar da ajiye aikinsa daga bugama Kasarsa bayan da Chile ta doke Argentina a bugun daga kai saimai tsaron gida a wasa karshe da akayi a COPA AMERICA Centenerio.
Dan wasan mai shekaru 29 yayi bakin kokarinsa a wasan Barcelona da Celtic daci 3_1 a wasan kasa da kasa na Champion Cup.
The post An bayyana Lionel Messi amatsayin dan wasanna musamman appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.