Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Sojoji sun kwato makamai a hannun Boko haram

0

Har yanzu rundunar sojan kasa bata yi kasa a gwiwa ba a yakin da take yi da kungiyar yan ta’adda da aka fi sani da suna Bokoharam, a kwanan ma rundunar ta kwato makamai a hannun yan Kungiyar.

Cikin wani sanarwa da mai magana da yawun rundunar Kanal Sani Kukasheka Usman yace sun kai samame ne bayan jama’an gari sun gulmata musu labarin ganin yan kungiyar a garin Gamboru, inda suka kwato makaman.

Kanal Sani ya bukaci jama’a da su cigaba da basu ingantattun labarai dangane da yayan kungiyar. A yayin samamen da aka kai da sassafe, rununar sojan ta gano makamai da suka hada da bindiga kirar AK guda biyar masu lambobi kamar haka AK-L-AGB 1172, AK-L PU2879, AK-56-2556688, AK-56-22622832 da AK-56-22622315. Sa’annan sun gano alburusai da bamabamai da dama.

Runudanr sojan kasarnan na mika godiyanta ga jama’an da suka gulmata ma sojoji labarin yan Bokoharam wanda ya kai ga kwato makaman. Wannan shine irin goyon bayan da muke bukata daga jama’an kasar nan wanda zai taimaka mana wajen kakkabe sauran yan ta’addan da suka rage.

Muna kara yin kira ga al’umma da su kara bude idanuwansu, kuma su lura da abubuwan dake faruwa a unguwanninsu, sa’annan da su kai rahoton duk wani mutum da basu gane mashi ba.

A wani labari makamancin wannan, rundunar sojan ta kau da wani jaka da ake tunanin cike yake da abubuwan fashewa da aka ajiye kusa da tsohon gwamnan jihar Borno. Usman yace an gano jakan ne a ranar lahadi 31 ga watan yulio lokacin da wani matafiyi ya ga jakan a kusa da gidan tsohon gwamna Mala Kachalla kuma ya kai kara ga hukumar Soja.

The post Sojoji sun kwato makamai a hannun Boko haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса