Mataimakin shugaban kasar Najeriya farfesa Yemi Osinbajo yayi kira ga yan Najeriya da sauran ma’aikatan gwamnati da su cigaba da kasancewa masu godiya da Allah a kowane hali suka samu kansu.
Yemi Osinbajo
Osinbajo yayi kiran ne a ranar Lahadi 31 ga watan yulio a garin Abuja a wani taron addu’a da aka shirya a cocin Living Faith dake jayi Abuja, cikin bukukuwan murnar zagayowar ranar ma’aikata. Osinbajo ya samu wakilicin Fasto Oluseyi Malomo shugaban cocin fadar shugaban kasa.
Osinbajo ya bukaci ma’aikatan kasar nan du su rika bin ka’idojin aiki sau da kafa da kuma yi wa shuwagabanni biyayya; “ba don ganin ido ba, sai don tsoron Allah”. Daga nan sai ya kara da janyo hankalin ma’aikata da su daina ganin tunanin wai suna ma wani mutum ne aiki, amma su rika ganin kansu a matsayin masu yi ma Ubangiji hidima, wanda shine zai musu sakayya.
Osinbajo ya bayyana tabbacin sa na cewa za’a samu wata kabila dake cike da mutane jajirtattu wadanda suke cike da son kasa Najeriya, kuma zasu yi iya kokarinsu wajen ganin sun kawo ma kasar nan ci gaba.
Fasto John Ugwu ya yi addu’o’i na musamman ga shuwagabannin kasar nan, bangarorin kasar da kuma ma’aikatan kasar. Ugwu ya bukaci mabiya addinin Kirista da su cigaba da bin addinin su sa da kafa, inda ya kara jaddada cewa haka ne kadai hanyar dacewa da rayu mai amfani duniya da lahira.
Bikin zagayowar ranar ma’aikatan na bana zai hado manyan ma’aikatun gwamnati da hukumomi tare da gudanar da sha’ani daban daban.Ana gudanar da bikin zagayowar ranar ma’aikatan ne duk shekara don tunawa da irin gudunmowa da ma’aikatan tarayya ke bayarwa.
Ускоряя эволюцию автомобильного интеллекта: Группа Geely и StepFun представляют совместную экспозицию на Всемирной конференции по искусственному интеллекту 2025 года
Аэрофлот вернулся к полетам по расписанию после сбоя в информационной системе
Карабахская земля горит под ногами оккупантов
Американский офицер призвал США купить у РФ Командорские острова за $15 млрд
Школьники из ЯНАО улучшили свои знания на олимпиадной смене в Подмосковье
В День парашютиста героем рубрики «Знай наших» стал сотрудник вневедомственной охраны столичного главка Росгвардии младший лейтенант полиции Александр С.
Легкоатлеты из Мордовии показали лучшие результаты мирового сезона на международных соревнованиях в Москве
«Краснодар» и московское «Динамо» проведут сегодня первые матчи в Кубке России