Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Ya kamata FG ta gudanar da bincike akan balle kurkuku- Bello

0

–Gwamnan Jihar Kogi, Abubakar Yahaya Bello, ya nemi gwamnatin tarayya data rantsar da hukuma da ta bincike akan abubuwan da suka faru akan balle kurkukun koton karfe..

–Gwamnan Jihar Kogi , Alhaji Yahaya Bello, ya nemi gwamnatin tarayya da ta kaddamar da wata Hukuma ta bincike abubuwan da ya tattari balle kurkukun da ya faru a gidan yarin koton karfe a Jihar Kogi.

Gwamnan ya bayyana bacin ransa akan abinda ya faru a gidan yarin a ranar asabar, 30 ga watan juli, 2016, kuma yace da alaman akwai hadin baki tsakanin yan kurkukun da wasu Tsageru a waje da suke zuwa su fitar da abokan su.

Mutane 13 ne aka bada rahoton cewa sun arce daga kurkukun Koton Karfe a Jihar Kogi . Wannan shine karo na 3 na balle kurkuku a gidan yarin koton karfe tsakanin shekaran 2010 zuwa 2016.

Gwamnan jihar daya je gidan yarin a fusace tare da kwamishanan ‘yan sandan jihar ,da diraktan jami’an DSS da wasu jami’an tsaro, basu samu daman shiga kurkukun ba. Gwamnan ya lashi takobin yin amfani duk daman da yake dashi wajen nemo gaskiyan al’amarin abin da ya faru tunda abin ya faru ne karfe 3 na dare amma ba’a fada ma jami’an tsaro ba sai misalin karfe 5 na safe.

KU KARANTA : An kama yan Kurkuku 6 da suka gudu

Zaku tuna cewan wasu masu garkuwa da mutane sanye da kayan sarki zuwa kurkukun koton karfe  ranan juma’a, za’a gurfanar da su a kotu ranan 1 ga watan satumba. Har yanzu ba’a sani ba ko akwai alaka da wadanda suka gudu.

A bangare guda, an kama wata jami’ar hukumar gidajen yari bayan a kama ta tana shigo da kayan maye zuwaga yan kurkukun  Kirikiri. Jami’ar ta musanta wannan zargin cewa bata yi ba.

 

The post Ya kamata FG ta gudanar da bincike akan balle kurkuku- Bello appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса