Nayi nadamar goyon bayan Sheriff-inji Fayose
Gwamna jihar Ekiti, baki abin magana Ayo Fayose ya bayyana cewa yayi nadamar goyon bayan Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban Jam’iyar PDP.
Gwamna Fayose
sa’annan yayi tsokaci dan gane da rikita rikitar da ta dabaibaye jam’iyarsu, inda yayi zargin wasu mutane da yin zagon kasa ga yunkurin sulhu da ake yi a jam’iyar tasu ta PDP, saboda tsabagen son kai.
Fayose ya fadi hakan ne lokacin da dan takarar kujeran shugaban jam’iyar PDP kuma tsohon shugaban gidan talabijin na DAAR Communication Cif Raymond Dokpesi ya isa jihar Ekiti don yakin neman zabe. “dole in fada muku gaskiya, na dau darussa daga abubuwan da suka faru a baya. Ba zan kara goyon bayan wani dan takara ba a bayyane.
“a matsayina na shugaban jam’iya a Jihar Ekiti, ina tabbatar muku da cewa ba ni da wani dan takara da nafi so, kuma ban taba yi ma mutane na zancen wani dan takara ba. “zamu bar al’amarin zaben nan a hannun ubangiji a wannan lokaci don ganin munyi ma kowa adalci. “na koyi darasi daga goyon bayan Ali Modu Sheriff, kuma na san laifina ne. idan da mun kyale shi ya kai ga kujerar, toh da Allah kadai yasan halin da zamu shiga a yau.
Shiko Dokpesi ya roki masu zabe dasu zabe shi don shugabantar jam’iyar, kuma ya daidaita jam’iyar. “wasu mutane suna zargin wai na janye wa dattijon jam’iyar mu Bode George takara. Toh bari in fada muku, a garin Ibadan aka haife ni, kuma na fahimci al’adun yarbawa sosai, don haka ina girmama dattijai. “amma bamu taba zama da Bode George ba akan zancen janye mai takara ba. Don haka ban janye ma kowa ba, saboda a yanzu muna bukatan yaro sabon jinni wanda keda kuzarin yin aiki. “na zagaye jihohi 17 na kasar nan duk a cikin sati guda, kuma har yanzu da karfi na”. inji shi.
Daga nan kuma sai Fayose ya soki shugaban kasa Buhari inda yake cewa gwamnatin sa zata bare. A wani faifan bidiyo da jaridar Vanguard ta samo, an gwamnan yana maganganun batanci akan shugaban kasa, inda ya kara da cewa duk wani gwamnatin da zata sa mai ido, sai ta wargaje.
The post Nayi nadamar goyon bayan Sheriff-inji Fayose appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.