Shugaban kasar Togo Gnassingbe ya ziyarci jihar Lagas
-Manyan jami’an gwamnati daga kasar Togo, zasu rako shugaban kasar a ziyarar da zai kawo jihar Lagas
-An kimanta matatar Dangote zata samar da bututun danyen mai 650,000 a ko wacce rana kuma zata zama daya daga cikin manyan matata a duniya
Shugaban kasar Togo Faure Gnaissinbe tare da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Ana sa ran shugaban kasar Togo Faure Gnassinbe zai kawo ziyara ga matatar Dangote dake unguwar Lekki Free Zone, karamar hukumar Lekki na jihar Lagas a gobe. Shugaban kasar zai samu tarba daga gwamnan jihar Lagas, Akinwumi Ambode a filin jirgin saman Murtala Muhammed Airport da karfe 7:45 na safiyar Talata domin ziyarar matatar.
Manyan jami’an gwamnati daga kasar Togo zasu rako shugaban kasar a ziyarar sa zuwa jihar Lagas domin ganin matatar na miliyoyin daloli.
KU KARANTA KUMA: Wani mutumin kasar Sin ya kashe kansa a jihar Lagas
Shahararen dan kasuwa, Aliko Dangote zai kewaya da shugaban kasar Togo haraban matatar domin hadin gwiwa tare da karamar kasar yammacin Afrika. Ana sa ran gwamnan jihar Lagas Akinwunmi Ambode zai tattauna tare da shugaban kasar Togo game da muhimmancin zuba hannun jari.
An kimanta Matatar Dangote zata samar da bututun danyar mai 650,000 a ko wacce rana kuma zai zamo daya daga cikin manyan matata a duniya. A kwannan nan, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo ya kai ziyara Matatar a Lekki inda ya bayyana cewa za’a kammala a farkon shekara ta 2019.
The post Shugaban kasar Togo Gnassingbe ya ziyarci jihar Lagas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.