Добавить новость
ru24.net
World News in Dutch
Август
2016

Ana ma tsageru luguden wuta daga sama

0

Kanun labarun jaridun Litinin 1, Agusta sun tattara ne kan fatattakar tsageru a kudu maso yamma da kuma rikicin kasafin kudi a majalisar wakilai. Hukumar sojojin sama ta Najeriya (NAF) ta zafafa hare-harenta dare da rana domin korar tsageru dake addabar mazauna kusa da rafukka a jihohin Ogun da Lagos domin korar da su.

rundunar sojojin sama

Wannan cewar jami’in watsa labarai da hudda da jama’a na hukumar ne Group Capt. Ayodele Famuyiwa, ga jaridar Punch, ranar Lahadi, Yuli, 31. Famuyiwa, yace NAF ta kara kaimi kan hare-haren ta ga tsagerun a matsayin share fage domin sojojin kasa su shigo su fatattaki ‘yan bindigar

Jaridar ta ruwaito cewa jiragen yakin sama sun yi ma sansanonin tsagerun da ke Fatola da Abuja luguden wuta, abinda ya gigita tsagerun suka gudu suka shige cikin daji, amma sojojin na sa ido kan su

Rikicin majalisar wakilai kan aringizo cikin kasafin kudi ya ci gaba yayin da shugaban kwamitin kasafin kudi wanda aka sauke Abdulmumin Jibrin yayi magana kan abin da ya Kira “cin rashawa a hukumance” kan majalisar.

KU KARANTA : Rundunar Sojin Najeriya sun fitittiki yan Boko Haram

A cewar jaridar The Nation, a wata hira da yayi ta tashar Channels Television, Jibirin na mai cewa “an takulo wani abu a majalisar, kuma wannan takula ce zamu yi amfani da ita mu kawo sauye-sauye a majalisar kasa. Ba wai kasafin kudi na majalisar ba, Wanda ake magana, wannan zai kawo gagarumin canji domin a kwai cin rashawa sosai a majalisar kasa”.

 

The post Ana ma tsageru luguden wuta daga sama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.




Moscow.media
Частные объявления сегодня





Rss.plus
















Музыкальные новости




























Спорт в России и мире

Новости спорта


Новости тенниса