Saida Ryan Giggs ya kusa bugun Ronaldo game da shan lemun kwalba
Ko shakka babu Cristiano Ronaldo na daya daga cikin yan wasan kwallon kafa masu kyaun jiki da kuma koshin lafiya. Wannan duka kau baya rasa nasaba da yadda shahararren dan kwallon na kungiyar Real Madrid yace kula da kansa da kuma lafiyar sa tun daga yawan motsa jiki da kuma yin hattara da abubuwan da yake ce na yau da kullum.
Wani labari da ya bayyana kuma a yanzu yana nuna cewa wannan halin nasa ya samo asali ne bayan da Ryan Giggs ya kusa dukan dan wasan tun yana dan shekara 18 bayan da ya gansa yana shan lemun kwalba na ‘koka kola’.
Ryan Giggs told ROnaldo never to drink a coke at breakfast
Shi dai dan wasan na dan asalin kasar Portugal ya koma kulob din Man Utd ne daga Sporting Lisburn tun yana dan shekara 18 inda ya ida gogewa tare da zama cikakken dan kwallon duniya kafin daga bisani ya koma kungiyar sa ta Real Madrid.
Labarin da ya tonu ne ta bakin wani makusancin yan wasan a sadda suna Man Utd din Aage Fjortoft da kuma Ole Gunner Solskjear wadan da suka ce a kwai wata rana da Giggs din ya shakari Ronaldo a bango bayan da ya gansa da lemun kwalba yana sha da safe.
A lokacin ne kuma sai Giggs din ya fada masa cewar kar ya kara sha.
Hakan kuma akayi don kuwa daga ranar Ronaldo bai kara shan lemun ba. Hakan kuma ko shakka babu ta taimaka masa sosai.
The post Saida Ryan Giggs ya kusa bugun Ronaldo game da shan lemun kwalba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.